An shawarci Tinubu ya ƙara harajin VAT

Saboda haka ƙarin ba zai shafi talakawa da masu ƙananan sana’o’i ba.

An shawarci Tinubu ya ƙara harajin VAT

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa na manufofi da tsare-tsaren kuɗi da sauye-sauye a haraji ya ba da shawarar ƙara harajin mai saye VAT.

Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya kuma ba da shawarar cewa za a sake duba tsarin raba kuɗaɗen shiga da harajin na VAT.

Ya yi magana ne a taron bayyana manufofin da tasirin hakan da kwamitin ya shirya.

Sai dai Taiwo ya kawar da fargaba kan nazari da shawarwarin da kwamitin ya gabatar, yana mai cewa hakan ba zai shafi talakawa da masu ƙananan sana’o’i ba.

Ana iya tuna cewa, a watan Fabarairun 2021 ne Gwamnatin Tarayya ta ƙara harajin VAT daga kashi biyar zuwa kashi 7.5 biyo bayan zartar da Dokar Kuɗi ta 2020.

Shugaban Kwamitin Harajin ya ba da tabbacin cewa ‘yan kasuwa ba za su ƙara farashin kayayyakinsu ba sakamakon ƙarin.

Ya ce, akwai buƙatar ƙara harajin mai sayen la’akari da yanayin tattalin arzikin Najeriya da muddin ba a zartar da shawarar ba jihohi da dama za su karye.

“Don haka muna buƙatar a ƙara harajin VAT. Za mu tabbatar da cewa ba zai shafi kasuwanci ba.

“Abin da kawai muke ganin karin ba zai shafa ba shi ne a kayan abinci da harkokin ilimi da kiwon lafiya da kuma muhalli.

“Saboda haka ƙarin ba zai shafi talakawa da masu ƙananan sana’o’i ba.

“Mun yi magana da ‘yan kasuwa game da lamarin kuma ba za su ƙara farashin kayansu ba.

“Muna so mu tabbatar idan muka yi gyara na harajin VAT, babu wanda zai ƙara farashin kayayyaki. Za mu zauna mu daddale komai da kamfanoni masu zaman kansu.”

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara