An shawarci ’yan Arewa a Kurmi kan neman ilim
Sarkin Hauswan Sapele Alhaji Sahabi Umar Sapele, ya yi kira da ba da shawara ga al’ummar Arewa su ba da himma a kan neman ilimi da kasuwanci.Sarkin ya yi wannan kiran ne a wajen taron yaye daliban makarantar Usman bin Affan Eyaen, ta kungiyar Izalatil Bidi’a Wa’ikamatis Sunna rashen Jihar Edo.“Da farko kira da shawarar […]
Sarkin Hauswan Sapele Alhaji Sahabi Umar Sapele, ya yi kira da ba da shawara ga al’ummar Arewa su ba da himma a kan neman ilimi da kasuwanci.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a wajen taron yaye daliban makarantar Usman bin Affan Eyaen, ta kungiyar Izalatil Bidi’a Wa’ikamatis Sunna rashen Jihar Edo.
“Da farko kira da shawarar da zan yi wa ’yan Arewa mazauna Kudu, musamman Jihar Delta da Edo game da hadin kai da kuma babban abin da ya zama wajibi mu himmatu a kan neman ilimi, domin sai da ilimi za mu samu ci gaba. Don haka ya kamata mu gane babu wata al’umma wadda ta taba shahara a cikin jihilci ko ta kafu ta samu ci gaba a cikin jahilci. Don haka shawarata gare ku, ku himmatu a kan neman ilimi da tura ’ya’yanku zuwa karatu.”
Da wannan ya mika sako zuwa ga daliban makarantar, inda yake cewa: “Ina kira ga daliban da aka yaye su yi aiki da abin da aka koya musu kuma su zama jakadu na kwarai. Su kuma iyaye su taimaka wa ’ya’yansu a kan zuwa su karo ilimi.”
Daga karshe, ya shawarci ’yan kasuwa cewa su kasance masu aiki da gaskiya da rikon amana. Ya ce su tsaida gaskiya da rikon amana domin kasuwanci akwai rufin asiri idan aka rike shi da gaskiya tare da tsoron Allah.