An shawarci ’yan Arewa mazauna Kurmi su hada kai

Mai martaba Sarkin Bare-Barin Jihar Legas, Alhaji Mustafa Mai Kanuri na Legas ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna Kurmi da su haɗa kansu su zamo tsinsiya  maɗaurinki ɗaya. Ya ce kowane ɗan Arewa baƙo ne a yankin Kudancin ƙasar nan, don haka ya zama wajibi su dinga kallon kansu a matsayin ’yan uwan juna […]

An shawarci ’yan Arewa mazauna Kurmi su hada kai

Mai martaba Sarkin Bare-Barin Jihar Legas, Alhaji Mustafa Mai Kanuri na Legas ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna Kurmi da su haɗa kansu su zamo tsinsiya  maɗaurinki ɗaya.

Ya ce kowane ɗan Arewa baƙo ne a yankin Kudancin ƙasar nan, don haka ya zama wajibi su dinga kallon kansu a matsayin ’yan uwan juna domin ci gaban kansu. “Mu ’yan Arewa a nan kudu dukkan mu guda ne sai dai kowa ya san daga inda ya fito kuma gargaɗin da zan yi mana shi ne, wannan kafa biyun da muke da su, su zamo ɗaya na gida Arewa ɗaya na nan Kudu. Kada mutum ya zo ya miƙe ƙafa ya manta daga inda ya fito, wajibi ne mu yi zumunci da ’yan uwanmu na Arewa,” inji shi.

Maikanurin ya bayyana haka ne a sa’ilin da ya naɗa sarkin Bare-Barin Jihar Ogun, Alhaji Muhammadu Gana, bikin naɗin da ya gudana a garin Shagamu a ƙarshen makon da ya gabata.

Ya shaida wa Aminiya cewa da yaddar Shehun Barno ya naɗa sarkin Bari-Barin na Jihar Ogun. Ya ce su a al’adarsu ta Kanuri, suna yin biyayya matuƙa ga shugabanninsu da ke Jihar Barno, don haka ba su yadda a yi wani naɗin sarautar Bare-Bari a Kurmi sai da izinin Shehun Barno.

Sabon Sarkin, Alhaji Muhammadu Gana wanda shi ne Sarkin Bare-Bari na farko a jihar ya shaida wa Aminiya cewa sama da shekara 70 da ta gabata iyayensu ke zaune a jihar amma Allah cikin ikonSa bai nufe su da samun sarautar ba sai a wannan lokacin.

Sakataren sarakunan Hausawan Jihar Ogun, Alhaji Inuwa, wanda ɗaya ne da daga cikin waɗanda suka jagoranci naɗin, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun kansu a haɗe yake kuma zaune suke lafiya da sauran ƙabilun yankin. “Kiran da zan yi wa al’ummarmu shi ne, kada mutum ya ɗau hukunci a hannunsa komai runtsi, domin yin hakan shi ke janyo tashin hankali. Idan akwai wata matsala sai mutum ya sanar wa shugabanni,” inji shi.

Bikin naɗin sarautar ya sami halartar sarkin Hausawan Abekuta, Alhaji Ibrahim Hassan da sauran sarakunan Hausawa jihar da jama’a da dama daga jihohin Legas da Ogun da Oyo da makamantansu.