An shawarci ’yan Arewa su mutunta kansu
Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Kurosriba, Hafiz Muhammad Inuwa ya nuna matukar bacin ransa game da yadda al’ummar Arewa mazauna fadin jihar suka bari wasu ke neman bata musu suna kuma wasu da ake zargi da zama barayin zaune. Ya ce shi ba kwamishinan ’yan Arewa ba ne kuma ba ya zo aiki Kurosriba domin […]

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Kurosriba, Hafiz Muhammad Inuwa ya nuna matukar bacin ransa game da yadda al’ummar Arewa mazauna fadin jihar suka bari wasu ke neman bata musu suna kuma wasu da ake zargi da zama barayin zaune.
Ya ce shi ba kwamishinan ’yan Arewa ba ne kuma ba ya zo aiki Kurosriba domin ya zame musu garkuwa ba ne, yadda wasu za su rika fakewa da dan uwansu ne kwamishina suna aikata miyagun halaye da suka saba wa doka. Don haka ya ja masu kunne da su kawar da wannan tunani kuma ya ce duk wanda aka kama da laifi, doka za ta yi aiki a kansa ba tare da nuna wannan dan wane ne ba.
Kwamishinan ya nuna bacin ransa ne lokacin da shugabannin kwamitin samar da zaman lafiya, tsaro da hadin kai da kuma ci gaba (PSU&P) suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, karkashin jagorancin shugaban kwamitin, Alhaji Ya’u Isma’il Girei a Talatar da ta gabata. Ya ce: “Magana ta gaskiya ba na jin dadin irin abubuwan da suke faruwa a unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri, domin wasu daga cikinku suna sane da maboyar masu aikata miyagun laifuka kuma suna zaune cikinku, ba ku iya sanar wa da jami’an tsaro ba.”
Ya ci gaba da cewa, “ina da labarin wasu daga cikinku suna sayen kayan sata a hannun barayi, sana’arsu ke nan; ba su da wata sana’a sai wannan. Ina tabbatar maku da cewa, duk Bahaushen da ’yan sanda suka kama shi da laifin sayen kayan sata, za a mika shi kotu kuma da shi da barawon za a yi masu tuhuma daya, domin barawon zaune ya fi na tafe. Idan babu barawon zaune, sauran barayi ma da sun daina.”
Daga nan sai ya shawarci al’ummar asalin Arewacin Najeriya mazauna Kurosriba da su mayar da hankali wajen gyara da kula da tarbiyyar ’ya’yansu kuma su rika tura su makaranta domin neman ilmin zamani da na addini.
Tun da farko, a jawabin da ya gabatar, shugaban kwamitin, Alhaji Ya’u ya nuna cewa makasudun kawo ziyarar shi ne domin neman hadin kai da jami’ansa wajen yaki da bara-gurbi da bata gari da suke shigowa Layin Bagobiri suna sajewa da ’yan unguwa suna aikata miyagun laifuka.
A karshe, Kwamishinan ya sha alwashin taimaka wa al’ummar idan suka taimaka wa jami’ansa wajen sanar da maboyar bata-gari. “Abin da mamaki da ciwo a ce kun zo daga Arewa, maimakon yadda ake ganin mutumin Arewa da daraja da mutunci amma kun bari wasu suna zubar maku da shi. Ya kamata ku tashi tsaye wajen yin duk abin da zai dawo maku da martabarku da darajarku.”