‘An shawo kan cutar Ebola a Najeriya da Senegal’

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kasashen Najeriya da Senegal sun shawo kan   annobar Ebola da ta yi ajalin fiye da mutum 2,800 a yankin Yammacin Afirka.Hukumar ta bayyana hakan ne ranar Litinin da ta gabata, inda ta ce ba a kara samun wani wanda ya kamu da kwayar cutar ba a kasar Senegal, […]

‘An shawo kan cutar Ebola a Najeriya da Senegal’
‘An shawo kan cutar Ebola a Najeriya da Senegal’

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kasashen Najeriya da Senegal sun shawo kan   annobar Ebola da ta yi ajalin fiye da mutum 2,800 a yankin Yammacin Afirka.
Hukumar ta bayyana hakan ne ranar Litinin da ta gabata, inda ta ce ba a kara samun wani wanda ya kamu da kwayar cutar ba a kasar Senegal, tun bayan rahoton bullarta a karshen watan jiya. Hakazalika, a Najeriya ma ba a kara samun labarin sabbin wadanda suka harbu da ita ba, tun bayan wanda aka samu a farkon wannan watan.
kwayar cutar tana kwashe tsawon kwana 21 ne a jikin wanda ya harbu da ita, kafin bayyanar alamunta. Kuma wannan na nufin har sai wadannan kwanakin sun cika ba tare da samun labarin sabon wanda ya kamu da ita ba, kafin  bayyana kasar a matsayin wadda ta shawo kan annobar.
Duka kasashe biyun da  hukumar ta bayyana, sun dauki tsauraran matakai ne wadanda suka hada da killace masu fama da cutar, da kuma bin sawun  duk wanda ya yi mu’amala da shi. Sai dai hukumomin kasashen Guinea da Laberiya da kuma Saliyo sun gaza wajen daukar irin wadannan matakan, abin da ya sa masana suke ganin ya sa annobar ta ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.  
A kasar Laberiya ne dai annobar tafi yin ta’adi, inda a can ta kashe fiye da mutum 1,500. Kodayake, a ranar 18 ga watan nan ne hukumar WHO ta bayyana cewa  adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai jumullar mutum 5,864 a kasashe biyar na Yammacin Afirka, inda kuma ta yi ajalin fiye da mutum 2,800 a baki dayan yankin.