An shawo kan rikicin da ya barke a Kasuwar Gidan Kwali
A ranar Alhamis ta makon jiya ne aka samu ɓarkewar rikici a kasuwar Gidan Kwali da ke Ojota a Legas. Rikicin, wanda a baya ake alaƙanta shi da na ƙabilanci a tsakanin Hausawan yankin da Yarabawa. Sai dai a zantawarsa da Aminiya, Sarkin Hausawan Ojota ya bayyana cewa rikicin ba na Hausawa da Yarabawa ba […]

A ranar Alhamis ta makon jiya ne aka samu ɓarkewar rikici a kasuwar Gidan Kwali da ke Ojota a Legas.
Rikicin, wanda a baya ake alaƙanta shi da na ƙabilanci a tsakanin Hausawan yankin da Yarabawa. Sai dai a zantawarsa da Aminiya, Sarkin Hausawan Ojota ya bayyana cewa rikicin ba na Hausawa da Yarabawa ba ne, illa dai kawai wadansu tsirarun zauna-gari banza ne suka haddasa shi, waɗanda kuma sanannu ne a yankin.
“Wadansu zauna-gari banza ne da suka zo suka tare a cikin kasuwar ta Gidan Kwali, su ba saye da sayarwa suke ba, sai dai kawai idan mutanenmu ’yan Arewa sun yi kasuwa sai a ba su wani kaso. A irin wannan zama ake yi tare da tsagerun, duk lokacin da aka yi kasuwa ana ba su na goro a haka muke zaune da su; kodayake hakan ba ya damunmu, ba kuma shi ne silar rikicin ba. Domin musabbin rikicin shi ne, wani ɗan kasuwa Bahaushe ne ya bai wa abokin kasuwancinsa ɗan ƙabilar Ibo Naira dubu 50 ya je ya sayo kayan gwangwan. Ko da ɗan ƙabilar Ibon ya karɓi kuɗin ya sayo kayan sai ya kawo kasuwar amma ya sayar wa wani mutum na daban. Da labari ya iske wanda ya ba shi kuɗin sai ya je ya same shi, sai jayayya ta ɓarke a tsakaninsu har ta kai ga sun fara doke-doke. To sai waɗannan Yarabawa ’yan ƙungiyar asiri suka yiwo kan Bahaushen, suka far masa da duka, suka fasa masa kwalba a kai jini ya rufe shi. To da haka rikicin ya soma,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Da ’yan kasuwar suka ga haka sai suka far wa ’yan ƙungiyar asirin. Nan take suka fi ƙarfinsu, suka kora su. Sai suka koma gefe suka yiwo gayya, akwai wani a cikinsu ana ce masa Ojo; shi ne ya raba musu bindigogi uku. Nan suka yiwo cikin kasuwar suna harbi a iska. Nan ma dai aka sake kora su to da taimakon Allah an sami jami’an tsaro sun shiga tsakani sun kuma tabbatar da tsaro. Jami’an tsaro a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas sun shirya tarurrukan zaman lafiya a tsakanin shugabanin kasuwar yankin da na ƙabilun yankin.