An shawo kan rikicin Majalisar Wakilai
Ga dukkan alamu an shawo kan takaddamar shugabanci a Majalisar Wakilai, bayan da rahotanni suka ce bangaren magoya bayan Shugaban Majalisar Yakubu Dogara ya amince ya mika kujerar shugaban masu rinjaye ga bangaren Femi Gbajabiamila. Majalisar dai ta fada cikin rudu ne bayan zaben Dogara a matsayin shugabanta sabanin matsayar Jam’iyyar APC wadda ta bukaci […]
Ga dukkan alamu an shawo kan takaddamar shugabanci a Majalisar Wakilai, bayan da rahotanni suka ce bangaren magoya bayan Shugaban Majalisar Yakubu Dogara ya amince ya mika kujerar shugaban masu rinjaye ga bangaren Femi Gbajabiamila.
Majalisar dai ta fada cikin rudu ne bayan zaben Dogara a matsayin shugabanta sabanin matsayar Jam’iyyar APC wadda ta bukaci a zabi Gbajabiamila.
Bayan rashin nasara Gbajabiamila jam’iyyar ta mika sunansa a matsayin shugaban masu rinjaye, bukatar da Dogara ya ki amincewa da ita.
Jaridar Premiuim Times ta ce sallama kujerar ta biyo bayan wata ganawa a tsakanin Dogara da wasu wakilan majalisar a gefe daya da kuma tsohon shugaban majalisar kuma Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Tambuwal a Abuja a ranar Talata da daddare.
Gwamnonin Jam’iyyar APC a makon jiya sun kafa kwamiti a karkashin jagorancin Gwamna Tambuwal don nemo mafita kan rikicin majalisar.
Wani dan majalisar da ya halarci ganawar ta Talata ya shaida wa Premium Times cewa ’yan majalisar sun nace cewa wajibi ne a tabbatar da “adalci wajen lura da rabon mukaman shugabannin majalisar.”
Ya ce “An samu matsaya kan yadda za a samu zaman lafiya tare da tafiya da kowane bangare a majalisar, inda aka mika kujerar shugaban masu rinjaye ga bangaren Gbajabiamila ya zabi dan takara.”
Sai dai ya ce “Lura da da bukatar tsarin mulki na samar da daidaiton wakilci da kuma tsarin raba daidan mukamai, wancan dan takara zai iya fitowa daga kowane shiyya amma ban da Arewa ta Gabas ko Kudu maso Yamma, wadanda suke da shugaba da mataimakin shugaban majalisar a yanzu haka.”
Majiyar jaridar ta ce, wakilan sun shaida wa Gwamna Tambuwal cewa, akwai kara a kotu da wakilan majalisar na Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya suka kai kan batun, kuma warware batun ta hanyar adalci da zai tafi da kowace shiyya ne kawai zai zamo abin karba.
Wani dan majalisar ya ce, sun yanke shawarar cewa idan aka kasa samun matsaya kan shugaban masu rinjaye, to zaben shugabannin majalisar za a warware shi ne ta hanyar gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci kamar yadda dokar majalisar ta tanada.