An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila
Hamas tana sake jaddada aniyar ci gaba da mutunta dukkan yarjejeniya da ka’idojin da aka gindaya.
![An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/thumbs_b_c_c9c8a3b172da42422c6dd20516462f53.jpg)
Hamas ta sanar da yanke shawarar jinkirta sakin fursunonin Isra’ila nan gaba har sai abin da hali ya yi.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta fitar tana mai cewa an ɗauki matakin ne a matsayin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi.
Sanarwar da ɓangaren sojin Hamas ɗin ya fitar ta ce “fiye da mako uku, shugabacin ƙungiyar na bibiyar yadda maƙiya suka gaza cika ka’idojin yarjejeniyar da suka cimma.
“Karya wannan ƙa’ida, har da jinkirta dawowar waɗanda suka rasa muhallansu zuwa Arewacin Gaza, inda ake fakon su tare da harbin su, da harba musu bama-bamai, a yankuna daban-daban na Gaza, wanda hakan ke nuni da yadda suka gaza ƙyale ayyukan jinƙai, da sauran yarjejeniyar da suka cimma tunda farko.
“Baya ga nan, dakarun na Hamas tun farko sun mutunta wannan alƙawari da aka yi.
Saboda haka Hamas ta ce “sakin ƙarin wasu masu rajin kafa ƙasar Yahudawa a ranar Asabar, 25 ga watan 2025, sun dakatar da shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran maƙiya, za su fara mutunta yarjejeniyar da aka cimma da aka fara aiwatarwa makonin da suka gabata.
“Muna sake jadada aniyarmu ta ci gaba da mutunta dukkan yarjejeniya da ka’idojin da aka gindaya, idan har masu mamayar suka bi su sau da ƙafa.
A shirye muke mu ɗauki mataki — Isra’ila
Tuni ita ma Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar da Hamas ta fitar ta dakatar da sakin mutanen da take garkuwa da su.
Sanarwa da Ministan Tsaron Isra’ila ya fitar ta ce “sanarwar dakatar da sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su ya saɓa yarjejeniyar tsagaita cimma wutar da ta musayar fursunoni da aka amince,” in ji Israel Katz.
“Na bai wa dakarun IDF umarnin kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana dangane da duk wani da ka iya biyo ba a Gaza domin kare al’umma.
“Ba za mu bari a maimaimata abin da ya faru ranar 7 ga watan Oktoba ba..” in ji Katz.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 23 a yau Litinin.
Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 48,180, inda a yanzu aka sauya alƙaluman zuwa 62,000 saboda an ayyana waɗanda suka ɓata a matsayin matattu.