An shiga ruɗani a kasuwar Wuse bayan arangamar ’yan sanda da ’yan shi’a

An yi arangama tsakanin ‘yan sanda da ‘yan shi’a a ranar Lahadi.

An shiga ruɗani a kasuwar Wuse bayan arangamar ’yan sanda da ’yan shi’a

An shiga ruɗani a kasuwar Wuse da ke Abuja, wanda hakan ya sanya ’yan kasuwa rufe shagunansu, yayin da kwastomomi suka dinga ficewa daga kasuwar.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya, bayan wata arangama da ta tsakanin ‘yan sanda da mabiya ɗariƙar shi’a, a kusa da kasuwar.

An tabbatar da mutuwar ’yan sanda biyu da wani ɗan kasuwa, yayin da ‘yan shi’a suka ce su ma sun rasa wasu daga cikin mabiyansu.

Rikicin na ranar Litinin ya samo asali ne sakamakon yunƙurin da hukumar gudanarwar kasuwar ta yi na dawo da wani jami’i da aka kora a matsayin sabon manajan kasuwar.

Usman Kamba, wani ɗan kasuwa a kasuwar, ya ce jami’an sun zagaya kasuwar a ranar Litinin, suna sanar da shirinsu na naɗa Musa, a matsayin sabon manajan kasuwar.

An zargi Musa da hura wutar tashin hankali ’yan watanni da suka gabata wanda ya kai ga ƙone wasu shaguna bayan wani jami’an tsaro da ke tare da kotun tafi-da-gidanka, ya harbe wani ɗan kasuwa.

Wani ɗan kasuwa, Bello Ahmad, ya ce wasu matasa sun fusata da jami’an, inda suka farmake su tare da yi musu dukan tsiya.

“An tura ‘yan sanda zuwa kasuwar don tabbatar da zauna lafiya. Duk da haka, dukkanin shagunan sun ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ƙarfe 2 na rana,” in ji Ahmad.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50