An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sanda

Alamu dai na nuna cewar akwai yiwuwar Obasa ya dawo kan muƙaminsa.

An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sanda

An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda.

An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba.

An maye gurbinsa da Mojisola Meranda, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar kai a majalisar da kuma jam’iyyar APC mai mulki a Jihar.

Rahotanni sun nuna cewa an matsa wa Meranda da ta sauka daga muƙaminta, bayan da ake zargin cewa Shugaba Bola Tinubu bai gamsu da sauke Obasa daga muƙaminsa ba.

A safiyar ranar Alhamis, labari ya bayyana cewa an janye wa Meranda jami’an tsaron da ke ba ta kariya.

A gefe guda guma an mayar wa jami’an da za su ba shi kariya, alamar da ke nuna ana shirin dawo da shi kan muƙaminsa.

Wata majiya ya shaida wa Aminiya cewa Obasa ya shiga zauren majalisa tare da ’yan sanda, yana ƙoƙarin shiga ofishin kakakin majalisar.