Murja Kunya ta yi layar zana daga gidan yari a Kano
Ana zargin Murja da koyar da karuwanci da bata tarbiyyar kananan yara.
Mutane da dama a Kano sun shiga rudani kan bacewar fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, daga gyaran hali a jihar.
Aminiya ta rawaito cewa Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gama PRP a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare matashiyar a gidan gyaran hali na Kurmawa.
- Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 10 a Ebonyi
- Kwastam ta kama manyan motoci 15 na kayan abinci a Sakkwato
A ranar Talatar da ta gabata ne, Hukumar Hisbah ta jihar, ta kama Murja bayan korafi da al’ummar unguwar Tishama, suka shigar na kokarin bata wa ’ya’yansu tarbiyya.
Bayan gurfanar da ita a gaban kotu, an zarge ta da koya wa kananan yara karuwanci da tada hankali.
Sai dai bayan karanto mata laifukan da ake zargin ta da su Murja ta musanta aikata laifukan.
Alkalin kotun, Mai sharia Nura Yusuf Ahmad, ya bayar da umarnin tasa keyarta zuwa gidan ajiya da gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2024 don yanke hukunci.
Alkalin ya dage shari’ar ne don duba yiwuwar bayar da ita beli a zaman kotun na gaba, kamar yadda lauyanta ya bukata.
‘Ba tserewa Murja ta yi ba’
Yayin da yake mayar da martani game da lamarin, mai magana da yawun kotunan Shari’ar Musulunci, Muzammil Ado Fagge, ya ce ba shi da masaniya game da gudun Murja daga gidan yari.
“Mu ma mun ji wannan labari cewa ta tsere daga gidan gyaran hali. Mu dai a iya saninmu alkali ya kai ta ajiya sannan kuma ya sa ranar 20 ga Fabrairu don duba yiyuwar bayar da belin ta ko akasin haka.
“Ba mu san abin da ya faru ba. Mun san abin da ya faru a kotu ba ya sauyawa, musamman a kan abin da ya shafi shari’a irin wannan wanda kuma ba shi ne na farko ba.
“An taba gurfanar da ita a gaban Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a fiilin Hockey a kan makamancin irin wannan laifin.
“Abin da muka sani shi ne Murja tana gidan yari. Amma ba zan yi mamaki ba idan aka ce an bayar da belinta.”
Da umarnin kotu muka sake ta —Gidan yari
Yayin da yake mayar da martani a kan wannan zargi mai magana da yawun gidan gyaran hali na Kurmawa, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya ce an saki Murja tun a ranar Alhamis.
A cewarsa: “Gidan ajiya da gyaran hali yana tafiya ne bisa dokoki. Wuri ne kamar banki da takarda yake amfani.
“Takarda ce take kawo mutum haka kuma takarda ce ke fitar da shi. Idan aka ce da wani kuskure to ba za a karba ba.
“Muna da sa hannun dukkanin alkalan da ke Jihar Kano. Dole sai Alkali ya sa maka hannu sannan za a kawo ka, haka ma dole sai ya sa hannu kafin a fitar da kai.
“Game lamarin Murja, babu wanda ya gudu daga gidan gyaran hali. Idan ka tsallake katanga a kokarinka na guduwa to harbin ka za a yi. Duk da cewa muna da kofofi da yawa amma muna da jami’an tsaro da ke gadin su.
“A takaice kotu ce ta kawo Murja, ita ce kuma ta fitar da ita.”
Abin da Hisbah ta ce
Hukumar Hisbah, wadda ta kama Murja, ta ce ita aikinta shi ne ta kama mutum, amma ba ta da hurumi kan yanke masa hukunci ko fada wa alkali irin hukuncin da zai yi masa.
Haka kuma Hisba ta ce wannan abu da ya faru ba zai sa ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Al’umma dai na ci gaba da lugudan labba musamman a shafukan sada zumunta kan wannan lamari.