An shiga rudani bayan rushe fadar basarake a Abuja

Mazauna yankin sun shiga kokwanta game da makomarsu a yankin.

An shiga rudani bayan rushe fadar basarake a Abuja

Al’ummar Jabi Masallaci da ke gundumar Jabi a Abuja, sun shiga rudani yayin da jami’an hukumar kula da tsaftar Babban Birnin Tarayya Abuja suka rushe fadar basaraken yankin a wani samame da suka kai a ranar Alhamis.

Wani mazaunin yankin Ayuba Kefas ya shaida wa Aminiya cewa rushe fadar abun damuwa ne ga ’yan asalin yankin domin a yanzu ba su da wurin da za su yi taro da ke bukatar kulawar basaraken.

Ya ce, “Wannan shi ne karo na farko da irin wannan abu ya taba faruwa, musamman rushe fadar wani basarake a duk wani kauye da ke cikin Babban Birnin Tarayyar.

Ya kara da cewa lamarin ya fi damun mazauna yankin game da makomarsu domin yanki ne da ke da daruruwan masu karamin karfi.

Sai dai kokarin jin ta bakin basaraken bai samu ba saboda an ce ya tsufa sosai kuma yana cikin kaduwa kan faruwar lamarin.

Aminiya ta rawaito cewa rundunar ta kunshi jami’an Sashen Ci gaban Babban Birnin Tarayya, DRTS, ’yan sanda, NSCDC, AEPB, da dai sauransu, wanda ke aikin rushe gine-ginen da ke ba bisa ka’ida ba.

Hukumomin sun ce da yawa daga gine-ginen da aka rushe bata-gari ne ke amfani da su a matsayin mafaka.

Zaɓen Edo: An fara ƙirga ƙuri’u

Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna

’Yan sanda sun kama mai yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Kaduna

Gwamnan Kano ya raba wa makarantu kujeru da tebura 73,000