An shigo da gurbataccen mai Najeriya —Majalisa

Majalisa ta kafa gwamnatin gaggawa domin bincika batun shigo da gurbataccen man dizel Najeriya daga kasar waje

An shigo da gurbataccen mai Najeriya —Majalisa

An ƙara farashin man fetur a Najeriya

Majalisar Dattawa ta gargadi ’yan Najeriya kan wani gurbataccen man dizel daga aka shigo da shi kasar daga kasashen ketare.

Sanata Asuquo Ekpeyong ya ja hankalin ’yan kasa cewa daga kasar Togo aka shigo da gurbataccen man bayan shigo man mai hatsari ga lafiyar dan Adam da kuma na’urori.

Da yake gabatar da kudirin a zauren Majalisar a ranar Laraba, Sanata Asuquo ya bayyana cewa ingancin man da ake zargi bai kai na wanda ake amfani da shi a Najeriya ba.

Ya shaida wa majalisar cewa tun ranar 16 ga watan Yuni jiragen ruwa 12 suka kai tan 660 na gurbataccen man dizel birnin Lome na kasar Togo.

Ya ce daga nan ne aka rarraba su zuwa kasashen Afirka, ciki har da Najeriya.

A cewar Sanata Asuquo, duk da hukumar kula da hakowa da kuma cinikin man fetur (NMDPRA) ta sauya dokokin nau’in man da ake amfani da shi, ba ta iya saka ido kan amfani da man a faɗin kasar.

Da yake tsokaci, Sanata Adams Oshiomhole ya bukaci majalisar ta kafa kwamitin gaggawa domin bincikar lamarin.

Oshiomhole ya ce hukunta masu hannu a irin wannan badakala shi ne zai kawo karshen yadda masu son zuciya ke jefa rayuwar ’yan Najeriya cikin hadari domin biyan bukatar kansu,

Oshiomhole ya kuma bayyana takaici bisa yadda hukumar ke ci gabada bayar da lasisin shigowa da man dizel daga kasashen waje, duk da cewa akwai matatun cikin gida da za su iya wadatar da kasar da man.

A karshen zaman Majalisar ta kafa kwamatin gaggawa don bincika man da ake shigowa da shi.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa