An shirya wa kansilolin Jihar Kaduna kwas a kasar Kenya domin taimaka musu wajen tafiyar da ayyukansu.
Shugaban kungiyar Kansilolin Jihar Kaduna Abubakar Ibrahim danyaro ne ya shida wa wakilinmu haka a farkon wannan makon jim kadan da dawowarsu daga Kenya. Shugaban wanda ya nuna godiyarsu ga gwamnatin Jihar Kaduna saboda shirya musu kwas na mako daya a Nairobin Kenya, ya ce horon da suka samu zai taimaka musu wajen tafiyar da […]
Shugaban kungiyar Kansilolin Jihar Kaduna Abubakar Ibrahim danyaro ne ya shida wa wakilinmu haka a farkon wannan makon jim kadan da dawowarsu daga Kenya.
Shugaban wanda ya nuna godiyarsu ga gwamnatin Jihar Kaduna saboda shirya musu kwas na mako daya a Nairobin Kenya, ya ce horon da suka samu zai taimaka musu wajen tafiyar da aikinsu na ’yan majalisar kananan hukumomi.
Malam danyaro ya ce gwamnatin Kaduna ta shirya musu kwas na kwan biyu a Kaduna kafin tashinsu zuwa kasar Kenya don sanin makaman Aiki, “Duk kwasa-kwasan da aka shirya mana za su taimaka don samun ci gaba mai ma’ana a yankunan karkara da ke kananan hukumominmu baki daya,” inji shi.
Ya nuna godiyar kungiyarsu ga gwamnatin jihar da shugabannin kananan hukumomi da ma’aikatansu saboda hadin kai da goyon baya da suke ba su.
Sai ya yi kira ga al’ummar Jihar Kaduna su ba Gwamna Mukhtar Ramalan Yero hadin kai da goyon baya domin su ci ribar mulkin dimokuradiyya.