An shirya wa manoma 300 bita kan noman zobo a Jigawa
Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da hadin gwiwar Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jihar Jigawa sun shirya wa manoman zobo bita a kan yadda za su inganta nomansa ta hanyoyin zamani. Kamar yadda shugabannin bangarorinn biyu suka bayyana wa manema a yayin bitar, sun ce nan ba da jimawa ba za a fara fita da […]
Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da hadin gwiwar Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jihar Jigawa sun shirya wa manoman zobo bita a kan yadda za su inganta nomansa ta hanyoyin zamani.
Kamar yadda shugabannin bangarorinn biyu suka bayyana wa manema a yayin bitar, sun ce nan ba da jimawa ba za a fara fita da zobo zuwa kasar Meziko da wasu kasashen duniya saboda muhimmancinsa.
Dokta Esigue, Babban Darakta ne a Ma’aikatar Gona ta Tarayya, wanda kuma shi ne ya jagoranci ayarin da ya shirya wa manoman zobon bitar, ya ce wannan kaddamarwa ce da aka fara da manoma 300 a jihar.
Ya ce manoman sun fito ne daga kananan hukumomin jihar 27, inda aka dauko mutum goma daga kowace karamar hukuma. “An shirya wa manoman ne bitar da nufin ilimantar da su a kan sana’ar noman zoborodo mai inganci da nufin kara wa manoman kwarin gwiwar ci gaba da noma shi,” inji Dokta Esigue.
Ya kara da cewar tuni kasar Meziko ta shirya da Najeriya domin fara fitar da zoborodon zuwa waje.
Daya daga cikin ’ya’yan kungiyar manoman zobo ta Jihar Jigawa daga Karamar Hukumar Kafin Hausa, Malam Aliyu Abdullahi Dumadumi Toka ya ce samar da kamfanin a Jigawa zai taimaka wa manoma wajen sayar da kayansu cikin sauki ya kuma bukaci manoma ’yan uwansa su guji aikata algushi a lokacin da suke zuba amfanin gonarsu a buhuna.
Haka kuma manomin ya yaba wa gwamnatin Jihar Jigawa bisa kokarin nemo wa manoman zobo kasuwa a kasashen ketare, yana mai cewa yin hakan ba karamin tallafi ba ne ga kananan ’yan kasuwa da manoman zoborodo da ke fadin Najeriya.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a kan yadda gwamnatinsa take kokari wajen farfado da Kasuwar Duniya ta Maigatari inda yanzu sama da kamfanoni 17 suka kama aiki gadan-gadan, kuma matasa yanzu suka zama masu dogaro da kansu a yankunan Gumel da Maigatari.