An soke aikin gyaran titi da aka ba kamfanin Dantata & Sawoe
Shekaru 12 da ba kamfanoni aikin gyaran titin amma sun kasa kammalawa
Gwamnatin Tarayya ta soke kwangilar gina titi da ta bai wa kamfanin Dantana & Sawoe daga Obajana a Jihar Kogi zuwa Benin a Jihar Edo.
Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta kuma soke kwangilar aikin da ta ba kamfanonin Mothercat Ltd, da kuma RCC Ltd.
Ministan Ayyuka, a cikin wata sanarwa ya ce, soke kwangilar ya zama dole saboda yadda kamfanonin ke tafiyar da ayyukansu cikin gazawa, sakaci da kuma rashin cika ka’idojin da aka yi yarjejeniya da su.
Sannarwar ta bayyana cewa, ayyukan da aka kwace su ne na mayar da na mayar da titin Obajana-Benin (Okene-Auchi) a Kogi da Edo Mai hannu biyu.
Mayar da babban titin Obajana – Benin, (Auchi-Ehor) a jihar Edo zuwa mai hannu biyu shi ne na biyu.
Na uku shi ne na mayar da titin Obajana zuwa Beni (Ehor – Benin) a Jihar Edo zuwa mai hannu biyu.
Ya bayyana cewa halayyar kamfanonin ta “ya hana kammala ayyukan a kan lokaci kuma hakan ya kai ga wucewar wa’adin aikin.”
Orji ya ce, “An ba da ayyukan tun ranar 3 ga Disamba, 2012, amma ’yan kwangilar suka yi watsi da su da gangan kuma ba su nuna aniyar kammala su ba.
“Hakan ya jefa masu amfani da hanyar cikin wahalhalu na tsawon lokaci saboda mummunan yanayin da hanyoyin suke ciki.”