An soke zaben ’yan majalisa biyu a Jihar Kaduna
Kotun Daukaka Kara ta Kaduna ta soke zaben ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna biyu da suka fito daga kananan hukumomin Kagarko da Sanga inda ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa ta sake gudanar da zabe a wasu rumfunan mazabun. Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan abokan hamayyar wadanda aka ce sun lashe zaben suka […]
Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jihar Kaduna
Kotun Daukaka Kara ta Kaduna ta soke zaben ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna biyu da suka fito daga kananan hukumomin Kagarko da Sanga inda ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa ta sake gudanar da zabe a wasu rumfunan mazabun.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan abokan hamayyar wadanda aka ce sun lashe zaben suka kalubalance su a kotun.
A ranar Talata ce kotun ta zartar da wannan hukunci, inda ta bada umarnin a sake zabe a wasu rumfuna 22 a kananan hukumomin biyu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce dan takarar majalisar a Jam’iyyar APC Mista Nuhu Shadalafiya ne ya kalubalanci nasarar abokin takararsa Mista Morondia Tanko na Jam’iyyar PDP a zaben ranar 9 ga Afrilun bana.
Tun farko Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar ta yanke hukuncin a sake zabe a rumfuna 22, amma sai Tanko na PDP ya daukaka kara don a dakatar da umarnin da kotun ta bayar. Sai dai Kotun Daukaka Karar ta yi watsi da wannan bukata tasa, tare da amincewa da hukuncin da kotun.
Hakazalika Kotun Daukaka Karar ta bada umarnin a sake zabe a Sanga, inda aka ayyana Madam Comfort Amwe ta Jam’iyyar PDP ta samu nasara.
Amwe ita ce mace kadai a Majalisar Jihar Kaduna, sai dai ta samu cikas ce, bayan da Alhaji Gambo Danga na Jam’iyyar APC ya kalubalanci nasarar da aka ce ta samu.