An soma ƙidayar ƙuri’u a Zaɓen Gwamnan Kogi

Akwai jihohi bakwai da ba su yin zaɓen gwamna tare da sauran jihohin a fadin tarayyar Najeriya.

An soma ƙidayar ƙuri’u a Zaɓen Gwamnan Kogi

Yadda ake lissafa ƙuri’u a rumfar zaɓe mai lamba ta 002 da ke unguwar Ugwolawo a Karamar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi

An soma ƙidayar ƙuri’u bayan rufe kaɗa ƙuri’a a hukumance a rumfunan zaɓe a birnin Lokoja na Jihar Kogi.

A rumfar zaɓe mai lamba ta 065 da ke yankin Sabon Gari, jami’an Hukumar Zabe ta Kasa INEC sun soma ƙidayar ƙuri’u bayan kammala tantance ƙirga ƙuri’un da aka kaɗa.

Haka ma lamarin yake a rumfar zaɓe mai lamba 067 da ke Otel ɗin Hukumar Yawon Buɗe ta Kogi.

Sai dai kawo yanzu ba a soma ƙidayar ƙuri’un ba a rumfar zaɓe mai lamba ta 012 da ke Kwalejin Crowder a yayin da ma’aikatan zaɓen ke ci gaba da tantance ƙuri’un da aka kada.

Daga nan ne kuma za a ɗauki ƙuri’un da sakamakon da aka samu zuwa mazaɓa, kafin a wuce zuwa ƙaramar hukuma.

‘’Yan takara 18 ne dai suka fafata a zaɓen na yau, sai dai ana ganin takarar ta fi zafi ne tsakanin manyan jam’iyyu uku da suka hada da PDP, APC da kuma SDP.

Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Asabar ce dai ake zaben gwamna a jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi.

Jihohin sun sauka daga layin lokacin da aka saba gudanar da babban zaɓe ne saboda hukunce-hukuncen kotu da ke ƙwacewa ko kuma su bayar da umarnin a sake zaɓe a jihohin.

Akwai jihohi bakwai da ba su yin zaɓen gwamna tare da saura a sun haɗa da Kogi, da Imo, da Bayelsa, da Edo, da Anambra, da Osun, da kuma Ekiti.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025