An soma biyan ma’aikata sabon albashi mafi ƙaranci a Adamawa

Ma’aikatan ƙananan hukumomi za su samu nasu ƙarin albashin a ƙarshen watan Satumba.

An soma biyan ma’aikata sabon albashi mafi ƙaranci a Adamawa

Ahmadu Fintiri

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya soma biyan sabon albashi mafi ƙaranci na N70,000 ga ma’aikata a jihar.

Matakin dai tabbatar da alƙawarin da gwamnan ya ɗauka ne a makon jiya wanda bayyana cewa zai fara biyan ma’aikata sabon albashin a ƙarshen watan Agusta.

Haka kuma, Gwamna Fintiri ya sha alwashin cewa ma’aikatan ƙananan hukumomi za su samu nasu ƙarin albashin a ƙarshen watan Satumba, wanda zai yi daidai da sabon albashi mafi ƙaranci da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar.

Majiyoyi da dama daga ma’aikatan gwamnatin jihar sun tabbatar da samun sabon albashin tare da bayyana farin cikin da suka tsinci kansu a ciki.

Da dama daga cikin ma’aikatan sun miƙa godiyarsu ga gwamnan bisa cika alƙawarin da ya ɗauka, suna masu cewa “ya tabbata mutum ne mai magana ɗaya.”

Ma’aikatan sun kuma yaba wa gwamnan kan farin cikin da ya sanya a zukantan iyalansu da ’yan uwa.

Kazalika, sun bayyana cewa za su ƙara hoɓɓasa wajen goyon bayan gwamnatinsa domin ci gaba da sharɓar romon dimokuraɗiyya.

Tabbatar da sabon albashi mafi ƙaranci ya ƙara ɗaga kimar Gwamnatin Fintiri da magoya bayansa ke cewa babu shakka ya yi abun a yaba.

 

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi