An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka
Bugu da ƙari China ta sanar matakin fara bincike a kan kamfanin fasaha na Google.
A bayan nan ne Amurka ta sanya harajin kashi 25 a kan kayayyakin da ake shigar wa ƙasar daga Canada da Mexico da kuma kashi 10 kan kayayyakin makamashi na Canada, yayin da kayayyakin China za su fuskanci harajin kashi 10.
Sakatariyar yaɗa labaran Fadar White House, Karoline Leavitt, ce ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
- Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo
- Hausawa sun yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri
Ta bayyana cewa “Canada da Mexico suna ba da damar shigar da muguwar ƙwayar nan ta fentanyl da ke kashe Amurkawa da kuma baƙin haure ba bisa ka’ida ba zuwa kasar mu.”
Ta ce Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin wanda zai soma aiki daga ranar Talata, domin magance matsalar shigar da maganin kashe raɗaɗi na fentanyl da matsalar ‘yan gudun hijira da ke shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba.
“Shugaba Donald Trump na ɗaukar ƙwararan matakai don kare Amurkawa daga matsalar maganin na fentanyl. Fentanyl shi ne kan gaba wajen sanadin mutuwar Amurkawa masu shekaru 18 zuwa 45,” in ji Leavitt.
Amurkan dai ta zargi masu safarar miyagun ƙwayoyi na Mexico da kasancewa “kan gaba a duniya wajen safarar” fentanyl da sauran ƙwayoyi, yana zargin akwai ƙawance tsakanin masu safarar da gwamnatin Mexico.
Game da Canada, Fadar White House ta yi ƙarin haske game da ƙaruwar samar da maganin na kashe raɗaɗi na fentanyl da kuma tsallaka wa da shi kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba, tana mai cewa: “an kama fentanyl a kan iyakar Arewa a bara wanda zai iya kashe Amurkawa miliyan 9.8.”
An soki China saboda zargin tana taka rawa wajen bayar da tallafi ga kamfanonin sinadarai wajen fitar da fentanyl zuwa ƙasashen waje, inda Fadar White House ta yi iƙirarin cewa: “ba wai kawai China ta gaza wajen daƙile tushen haramtattun ƙwayoyi ba, har ma tana taimaka wa wannan kasuwanci.”
Martanin Canada da Mexico
Ƙasashen Canada da Mexico sun sanar da ɗaukar matakan ramuwar gayya kan harajin da Shugaba Trump ya ɗora wa kayayyakinsu.
A ranar Asabar, Firaminista Justin Trudeau ya ce Canada za ta sanya harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka da suka kai dala biliyan 106.5 a matsayin martani ga harajin Amurka.
Harajin dala biliyan 20 zai fara aiki daga ranar Talata, sannan na dala biliyan 86 zai fara aiki a cikin kwanaki 21, kamar yadda Trudeau ya shaida wa wani taron manema labarai.
Trudeau ya yi gargaɗin cewa harajin zai cutar da Amurka, wacce daɗaɗɗiyar ƙawar ƙasar ta Canada ce.
Ya nemi mutanen Canada su riƙa sayen kayayyakin da aka yi a ƙasar, kuma su riƙa gudanar da hutu a gida maimakon a Amurka.
Ya ce ana kuma duba wasu matakan da ba na haraji ba, da suka haɗa da wasu da suka shafi ma’adanai masu mahimmanci da sayen makamashi da sauran ɓangarorin haɗin gwiwa.
Trudeau ya kuma ƙara da cewa, ƙasashen Canada da Mexico suna aiki tare don fuskantar harajin da Washington ta ɗora wa kayayyakinsu.
Fadar White House ta ce manufar harajin ita ce matsa wa Mexico da Canada da China lamba su ƙara ba da haɗin kai kan daƙile shigar da miyagun ƙwayoyi da tsaron kan iyakoki da hana kwarar baƙin haure shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya.
China ta bi sahu
China a wani mataki na ramuwar gayya ta lafta wa Amurka harajin kaso 15 cikin 100 na kayayakin kwal da na makamashin gas da ake shigar da shi kasar daga Amurka.
Ƙarin harajin a cewar Ma’aikatar Kuɗin Beijing zai fara aiki ne a makon gobe.
A cikin sanarwar da ta fitar ta ɗaukar matakan ramuwa, China ta zargi Amurka a ƙarƙashin Donald Trump da karya ƙa’idojin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
“Gaban kai da Amurka ta yi ita kaɗai ta lafta haraji ya saɓa ƙa’idojin Hukumar Kasuwaci ta Duniya. Wannan ya saɓa wa yarjeniyoyin kasuwanci da tattalin arziƙi tsakanin China da Amurka.”
Bugu da ƙari China ta sanar matakin fara bincike a kan kamfanin fasaha na Google.