An tabbatar da ingancin rigakafin Coronavirus a China

Masana sun tabbatar da ingancin rigakafin cutar coronavirus da aka samar a kasar Sin.

An tabbatar da ingancin rigakafin Coronavirus a China

Rigakafin Coronavirus

Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya, sun tabbatar da ingancin rigakafin cutar Coronavirus da aka samar a kasar Sin.

Sai dai duk da tabbacin da masanan suka bayar, sun ce akwai bukatar a yi kirdadon rigakafin ta tsallake matakin gwaji na uku da ake shirin yi a kanta.

Cikin rahoton da jaridar BBC ta wallafa, ya ce a halin yanzu rigakafin ta shiga matakin karshe na gwajin bayan tsallake mataki na daya da na biyu.

Rahoton ya ce cibiyar samar da magunguna ta Beijing Institute of Biological Products ce ta samar da rigakafin kuma ta fara aka fara amfani da ita China.

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya WHO sun nuna cewa, mutum 38,619,674 suka kamu da cutar a fadin duniya ciki har da mutum 1,093,522 da suka riga mu gidan gaskiya.