An tabbatar da mutuwar mutum 21 a harin garin Bassa na Filato

Kimanin mutum 21 aka tabbatar an kashe kuma mutum biyu suka samu munanan raunuka biyo bayan harin da aka kai a ranar Litinin a kauyen Zir-shi Maiyanga kusa da Dundu da ke yankin Kwall da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato   Harin ya auku ne awanni kadan kafin a gudanar da binne mutanen […]

An tabbatar da mutuwar mutum 21 a harin garin Bassa na Filato

Kimanin mutum 21 aka tabbatar an kashe kuma mutum biyu suka samu munanan raunuka biyo bayan harin da aka kai a ranar Litinin a kauyen Zir-shi Maiyanga kusa da Dundu da ke yankin Kwall da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato
 
Harin ya auku ne awanni kadan kafin a gudanar da binne mutanen da aka kashe makon da ya gabata a kauyukan da ke yankin Miango na karamar hukumar Bassa.
 
Harin daren ranar Litinin da aka kai kauyen Zir-shi Maiyanga ya auku ne da misalin karfe 10 zuwa 11 na dare inda ake zargin fulani makiyaya dauke da bindigogi suka kai.
 
Mai magana da yawun rundunar soja da ake yi wa lakabi da turanci “Operation Safe Haven”, Manjo Adam Umar ya ce Sarkakiyar yankin ce ta sanya jami’an soja  ba su isa wurin ba har sai bayan da wadanda suka kai harin suka gudu amma an samu gawarwaki sannan wani mutum guda kuma ya mutu a asibiti.