An tabbatar da nadin sabon Aare Musulmi na kasar Yarabawa

Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya tabbatar da nadin Alhaji Dawud Makanjuola Akinola a matsayin sabon Aare Musulmi na kasar Yarabawa da jihohin Edo da Delta. Sakataren Majalisar, Farfesa Ishak Oloyede, shi ne ya wakilci Sarkin Musulmin a wajen mika satifiket da kayan aiki […]

An tabbatar da nadin sabon Aare Musulmi na kasar Yarabawa
An tabbatar da nadin sabon Aare Musulmi na kasar Yarabawa

Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya tabbatar da nadin Alhaji Dawud Makanjuola Akinola a matsayin sabon Aare Musulmi na kasar Yarabawa da jihohin Edo da Delta.

Sakataren Majalisar, Farfesa Ishak Oloyede, shi ne ya wakilci Sarkin Musulmin a wajen mika satifiket da kayan aiki ga Alhaji Dawud, wanda ya gaji Aare Musulmi na farko a kasar Yarabawa, marigayi Alhaji Abdul-Azeez Arisekola Alao.
An gudanar da bikin tabbatar da nadin sabon jagoran al’ummar Musulmi ne a birnin Ibadan a ranar Asabar da ta gabata bayan amincewa daga Majalisar Limamai da Malamai (RABITAH) ta jihohin  Kudu maso Yamma da Edo da Delta.
Mai masaukin baki, Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ne ya wakilci shugaban taron Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a yayin da Gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola ya jagoranci wasu manyan mukarrabai da attajiran Musulmi maza da mata zuwa wajen taron. daruruwan limamai da malamai sanye da alkyabba da rawani da suka fito daga sassan Kudu maso Yamma ne suka halarci taro na yini daya.
Cikin sakonsa da Farfesa Ishak Oloyede ya karanta, Sarkin Musulmi ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dawo da koyar da ilimin addinin Musulunci da na Kirista a manhajar makarantun sakandare na kasar nan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen koyar da kyawawan dabi’u ga matasa. Ya ce akwai bukatar a hanzarta tilasta koyar da addini a  makarantun kasar nan.
Ya nemi sabon Aare Musulmin ya yi koyi da marigayi Alhaji Abdul-Azeez Arisekola Alao ta fannin yin amfani da dukiya da ilimi da dabaru da wayewarsa wajen ganin an samu kyakkyawar dangantaka a tsakanin Musulmin yanki da na sauran sassan kasar nan da kuma daukaka kalmar Allah a tsakanin al’ummar Musulmi da ke zaune yankin.
Cikin jawabin sabon Aaren ya ce zai yi aiki kafada-da-kafada da Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci ta Najeriya, domin yada Musulunci a sashin Yamma da kasa baki daya. Ya yi alkawarin zai yi amfani da wannan matsayi wajen koyi da salon jagoranci da marigayi Arisekola Alao ya yi amfani da shi a lokacin yana raye, inda sunansa ya yi fice a ciki da wajen Najeriya wajen taimakon Musulunci.
Sai dai ya ce, samun cimma wannan buri ya danganta ne da irin goyon bayan da ya samu daga Majalisar Limamai da Malamai da dukkan attajiran Musulmi, musamman masu rike da matsayin shugabanci da shugabannin kungiyoyin Musulmi daban-daban domin tsira a tare, inji shi.