An tabbatar da yin garkuwa da Basarake a Abuja
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da Sarkin garin Rubochi Alhaji Ibrahim Pada da ke karkashin Karamar Hukumar Kuje ta Abuja. Jami’in ofishin ‘Yan sanda na garin SP Michael Ada, ya tabbatar da sace Basaraken a daren ranar Talata, inda suka yi amfani da bindiga […]
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da Sarkin garin Rubochi Alhaji Ibrahim Pada da ke karkashin Karamar Hukumar Kuje ta Abuja.
Jami’in ofishin ‘Yan sanda na garin SP Michael Ada, ya tabbatar da sace Basaraken a daren ranar Talata, inda suka yi amfani da bindiga wajen fitar da Basaraken daga dakinsa sannan suka yi gaba da shi.