An tabbatar wa Idris kujerar Sufeto Janar
Hukumar Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya (NPC), ta tabbatar da nadin Ibrahim Idris Kpotum a matsayin cikakken Sufeto-Janar na ’Yan sanda.An tabbatar da nadin nasa ne a shekaranjiya Laraba a yayin taron Majalisar Zartarwa ta kasa da aka gudanar a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Taron dai ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban kasa, […]
Hukumar Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya (NPC), ta tabbatar da nadin Ibrahim Idris Kpotum a matsayin cikakken Sufeto-Janar na ’Yan sanda.
An tabbatar da nadin nasa ne a shekaranjiya Laraba a yayin taron Majalisar Zartarwa ta kasa da aka gudanar a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Taron dai ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari ya nada Idris ne a ranar 21 ga watan Yunin bana, a matsayin Sufeto-Janar na riko, bayan da Solomon Arase ya yi ritaya.
A yayin da yake bayani ga ’yan jarida a Gidan Gwamnati, jim kadan da kammala taron, Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya ce kusan kowa ya amince da nadin Idris, wanda haka ya sanya aka tabbatar masa da mukamin Sufeto Janar. Ya kara da cewa, mafi yawan bayanan da suka samu game da shi na yabo ne, cewa shi mutum ne nagari, don haka ana da yakinin zai gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
“Mun yi amanna da cewa Sufeto Janar mutum ne mai gaskiya da adalci kuma mun yi amanna da cewa zai ci gaba da nuna wadannan halaye na gaskiya domin yi wa kasa aiki yadda ya kamata,” inji Badaru.
Shi kuwa Gwamnan Legas, Akinwumi Ambode, cewa ya yi, duk da cewa an tabbatar wa Idris mukamin nasa, akwai kuma bukatar a mika wa Majalisar Dattawa, domin su tabbatar da shi.
A wani labarin makamancin haka kuma, Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da nadin kwamishinonin zabe na kasa na Hukumar Zabe (INEC).
Wadanda aka nada sun hada da Mohammed Haruna (Arewa ta Tsakiya) da mai Iya Mashal (mai ritaya) Ahmed Tijjani Mu’azu (Arewa maso Gabas) da Injiniya Abubakar Nahuce (Arewa maso Yamma) da Farfesa Okechukwu Ibeano (Kudu maso Gabas). Sai May Agbamuche Mbu (Kudu maso Kudu) da Dokta Adekunle Ladipo Ogunmola (Kudu maso Yamma).
Haka a yayin taron, an amince da nadin kwamishinoni biyar na Hukumar kidaya ta kasa (NPC). Wadanda aka nada sun hada da Dokta Eyitayo Oyetunji (Oyo) da Barista Patricia Iyaya (Binuwai) da Injiniya Benedict Ukpong (Akwa-Ibom) da Dokta Halu Bala (Kebbi) da kuma Gloria Isofo (Bayelsa).
Taron majalsar ya samu halartar tsofaffin shugabannin kasa Goodluck Jonathan da Janar Abdulsalami Abubakar da Chif Ernest Shonekan da Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Dabid Lawal. Haka kuma ya samu halartar gwamnonin jihohi da dama da suka hada da na Borno da Yobe da Ribas da Sakkwato da Abiya da Katsina da Kaduna da Taraba da Enugu da Legas da Kwara da sauransu.