An tabbatar wa kasar Kamaru mallakar tsibirin Bakasi

Yarjejeniyar Green Tree ta kawo karshe a ranar 15 ga watan Agustar bana, inda kasar Kamaru ta karbi mallakin tsibirin Bakassi 100 bisa 100. Kuma an tsara komai a cikin yarjejeniyar ta Green Tree, wadda ta bukaci Kamaru ta fara kyautata halin rayuwar jama’ar da ke zaune a tsibirin a cikin wa’adin shekaru biyar, tun […]

An tabbatar wa kasar Kamaru mallakar tsibirin Bakasi
An tabbatar wa kasar Kamaru mallakar tsibirin Bakasi

Yarjejeniyar Green Tree ta kawo karshe a ranar 15 ga watan Agustar bana, inda kasar Kamaru ta karbi mallakin tsibirin Bakassi 100 bisa 100. Kuma an tsara komai a cikin yarjejeniyar ta Green Tree, wadda ta bukaci Kamaru ta fara kyautata halin rayuwar jama’ar da ke zaune a tsibirin a cikin wa’adin shekaru biyar, tun kafin yankin ya zama mallakinta.
daukacin kashi 90 cikin 100 na al’ummar da suke rayuwa a wannan tsibirin duk ‘yan asalin Najeriya ne. Dangane da haka zabi ya rage a garesu da su zama ‘yan Kamaru wadanda suke rayuwa a kasarsu, ko kuma ‘yan Najeriya masu rayuwa a Kamaru, ko kuma su kaurace wa yankin. Amma dai Gwamnatin Kamaru ba ta tilasa musu yin zabi daga cikin wadannan matsayin ba. Sai dai wanda ya nufi ci gaba da kasancewa dan Najeriya, daga yanzu zai soma biyan takardar izinin zaman kasa.
Wadanda kuwa suka zabi zama ‘yan Kamaru za a buga musu takardar shaidar zama ‘yan kasa. Amma kuma su da ‘yan Najeriya gabaki dayansu za su fara biyan haraji na irin sana’o’in da suke yi. Sai dai abin tambaya a nan shi ne shin mutanen da sana’arsu kamun kifi ce kawai za su iya samun isassun kudin biyan takardar samun izinin zaman kasa ? Gwamna Okalia Bilai na Lardin Kudu maso Yamma, cewa ya yi a duk tsawon shekaru biyar da aka bai wa Gwamnatin Kamaru kyautata rayuwar jama’a a wannan yankin, ta wayar musu da kaikan yadda makomarsu za ta kasance, har idan wa’adin shekaru biyar suka cika.
A ranar 10 ga watan Oktobar 2002 ne Kotun duniya ta mallaka wa Kamaru tsibirin Bakassi, bayan takaddamar da Kamaru da Najeriya suka rika yi game da wannan yankin. Lamarin da ya kai su ga zuwa gaban kotu a birnin Hague, inda har bayan shekaru takwas ne aka zartar da hukunci. Kuma Najeriya ta dade tana ta takaddama akan cewa wannan tsibirin mallakintane tun shekara ta 1981. Sa’annan kuma a ranar 28 ga watan maris na shekara ta 2013, Hukumomin Najeriya karkshin jagorancin Minista Muhammed Bello Adoke da kuma tawagar Kamaru wadda Minista Dion Ngute ya shugabanta, hadi da wasu tawagogi na kasashen jamus, Amurka da kuma Faransa wadanda suka shaida sa hannu akan yarjejeniyar Green Tree, inda suka halarci wani taro na Hukumar kula da tabbatar da wanzuwar yarjejeniyar a karo na 21 a birnin Geneba.