An tada yamutsi a wajen zaben fidda gwanin PDP a Kuros Riba
An yi yamutsi a zaben wakilan ’yan takara da aka gudanar ranar Litinin a wasu jiohi da aka rusa zaben bisa zarge-zargen tafka magudi da kuma dauki dora a Kuros Riba ma an gudanar, musamman mazabar shiyya ta daya wadda zaben ke cike da takaddama da yada rade-radin soke zaben . A wancan zaben da […]
An yi yamutsi a zaben wakilan ’yan takara da aka gudanar ranar Litinin a wasu jiohi da aka rusa zaben bisa zarge-zargen tafka magudi da kuma dauki dora a Kuros Riba ma an gudanar, musamman mazabar shiyya ta daya wadda zaben ke cike da takaddama da yada rade-radin soke zaben . A wancan zaben da aka gudanar na wakilan jam’iyyar PDP ta ki nuna gamsuwar ta game da zaben saboda ganin cewa wasu daga cikin ’yan lelen ta ba su kai banter ba,sai aka soke zaben.
’Yan takarar zama wakilan masu takara shida ne suka fafata a wanna karo, inda mutum uku suka fito aka fafata, yayin da sauran mutane uku suka janye, kuma ma ba a ga keyar su ba a filin zaben ko wani wakilinsu.
Adamu Muhammad Baba, wato Adamun Master shi ne dai ya sake zama zababben wakilin ’yan takara a shiyyar mazaba ta daya da yawan kuri’u 170. Sai kuma Aishatu Halliru, wadda ita ma a wancan zaben ta lashe shi, wannna karon ma ta sake samun nasara da yawan kuri’u 94. Shi kuma Ndubuisi Nwafor, wanda a wancan karo shi ma masu goyon bayansa suka tsaya kai da fata sai ya samu nasara, a wannan zaben ya kai bantensa da yawan kuri’u 104. Hakan ya nuna mutane ukun kowa ya samu nasara ba tare da wata hamayya ba, saboda sauran abokan neman wakilicin uku ba su fito ba, ko ma su nuna za su sake fitrowa filin daga a yi da su.
Bayan kammala zabukan da aka yi na wakilan ’yan takara a fadin Kuros Riba, jam’iyyar PDP ta jihar ta nuna matukar gamsuwa da yadda sakamakon ya zo mata da kuma amincewa da duk wanda ya samu nasara.
Da Aminiya ta samu labarin rikici ya barke a yankin karamar Hukumar Kalaba ta Kudu, a wata mazabar har an jikkata wasu yayin da a karamar Hukumar Akamkpa ma sai da aka gayyato ’yan sanda da ke unguwar gidajen gwamnati mallakar jiha suka raka wadanda suka gudanar da zaben ganin yadda aka yi musu ca! Za a barke da fada an kwashe tsawon wuni magoya bayan Adamu Baba suna zagayawa ana murnar wannan nasara .
Daga bisani Adamu Muhammad Baba ya gode wa al’ummar Arewa mazauna Kalaba da suka fito suka sake mara masa baya ya sake samun wannan nasara .