‘An tafka ruwan da ba a taba yin irinsa ba a Katsina cikin shekara 100’

Ruwan ya kai kaso daya bisa ukun wanda ake samu a Nguru a shekara daya.

‘An tafka ruwan da ba a taba yin irinsa ba a Katsina cikin shekara 100’

Saukar ruwan sama mai karfi

Bincike ya nuna cewa wani mamakon ruwan sama da aka tafka a rana daya a birnin Katsina shi ne irinsa mafi yawa a tarihi cikin shekaru 100 da suka gabata.

A cewar Hukumar Harsashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), yawan ruwan da aka samu ya kai kusan milimita 100, inda ta ce wannan shi ne kololuwar adadin da za a iya samu a Arewacin Najeriya, kuma shi ma yana tafe da barazanar ambaliya.

Babban Darktan hukumar, Farfesa Mansur Bako Matazu ne ya bayyana hakan yayin wani taron kara wa juna sani da hukumar ta shirya a Abuja.

Ya ce, “A baya, mun yi harsashen cewa tsakanin watan Yuli da Satumban 2021, za a sami karuwar ruwan sama matuka, wanda zai shafi yankuna da yawa, har ma ya haddasa karamar ambaliya a wasu wuraren.

“A Jihar Katsina alal misali, bincikenmu ya nuna cewa an sami kusan milimita 100 na ruwan sama a rana daya. Ba a taba samun irin haka ba a cikin shekara 100. Hakan na nuna cewa ana samun sauyin yanayi sosai.

“Tsaka-tsakin ruwan da aka fi samu a rana daya shi ne milimita 100. Wannan fa kusan daya bisa ukun ruwan da ake samu a garin Nguru ne na Jihar Yobe, kuma daya bisa shida na wanda ake samu a Katsina a shekara daya, amma aka yi shi a rana daya.

“Hakan na dauke da babbar barazana kamar ta ambaliya, zaizayar kasa da kuma zaftarewar gabar kogi a wasu lokutan,” inji shi.

Da yake tsokaci a kan yuwuwar samun ambaliya a wasu Jihohin Arewa, shugaban hukumar ya ce, “Ana karkasa yanayi ne zuwa gida uku, kuma yanayi na ‘C’ shi ne ake samu a Arewa, wanda shi kuma ya kasu zuwa C1 da C2 da kuma C3. Dalilin da yasa kenan ake tafka ruwa sosai a bana.

“Muna fuskantar karin ruwan sama sosai a Katsina da Bauchi da Kaduna da Abuja da kuma Neja da ma wasu sassan na Arewa. Yawancinsu na fuskantar karin ruwan, mun fi fuskantar barazana yanzu fiya da a ko yaushe,” inji Farfesa Matazu.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja