An takaita jana’izar AGF AbdulRazaq ga iyalai kadai
Masu son jin yadda aka yi jana’izar na iya sauraro kai tsaye ta gidan radiyon Kwara FM
Iyalan Tsohon Antoni Janar na Tarayya, AbdulGaniyu Folorunsho Abdul-Razaq, mahaifin Gwamnan Jihar Kwara, sun ce iyalansa ne kadai za su halarci jana’izarsa.
Sun ce hakan ya zama wajibi saboda yanayin da ake ciki na cutar coronavirus da ke bukatar takaita taruwar jama’a.
“Saboda matsayinsa a Najeriya, mun san mutane za su so halartar jana’izar, amma mun zabi mu takaita ta zuwa ga iyalai kadai”, inji sanarwar.
Sun bukaci mutane su yi hakuri da halartar jana’izar domin kare lafiyar jama’a baki daya.
“Masu son sanin yadda jana’izar za ta kasance na iya sauraro kai tsaye ta gidan radiyo na Kwara FM 99.1FM.
Sanarwar da Dakta Alimi AbdulRazaq ya fitar a madadin iyalan mamacin ta yi godiya ga masu ta’aziya da taya su alhinin rashin mamacin wanda ake binnewa a Ilorin.