An tallafa wa fursunoni a Kirikiri da Ikoyi

kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah, reshen Agege a Jihar Legas ta kai tallafin kayan abinci da suturu ga fursunoni da ke zaman kaso a gidajen yari na Kirikiri da Ikoyi a Legas.Tallafin ya kunshi buhunan shinkafa da katon-katon na taliya da doya da dankali da man gyada da kayan miya da suturu sababbi da […]

An tallafa wa fursunoni a Kirikiri da Ikoyi
An tallafa wa fursunoni a Kirikiri da Ikoyi

kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah, reshen Agege a Jihar Legas ta kai tallafin kayan abinci da suturu ga fursunoni da ke zaman kaso a gidajen yari na Kirikiri da Ikoyi a Legas.
Tallafin ya kunshi buhunan shinkafa da katon-katon na taliya da doya da dankali da man gyada da kayan miya da suturu sababbi da tsofaffi da magunguna da kayan masarufi da aka kashe kudi fiye da Naira miliyan 3 wajen sayensu.
“An samu kudin ne daga jama’a Musulmi da suka bayar da gudunmawa daga masallatai daban-daban kuma tallafin na bana shi ne irinsa na 8 da kungiyar ta saba kai wa duk shekara a gidajen yari a cikin irin wannan wata na Ramadan,” inji Shugaban kwamitin masallacin Lawan Atana a Agege, Alhaji Umar Lawan Atana, wanda ya jagoranci malamai da shugabannin kungiyar da ’yan agaji zuwa mika wannan kaya ta hannun manyan jami’an kula da gidajen yarin.
Bayan kammala ziyarar gidajen yarin na yini 2, Alhaji Umar ya yi wa Aminiya bayanin cewa: “Saboda darajar wannan wata na Ramadan muka kafa kwamitin neman taimakon kudi da abinci da suturu da muke kai wa ga fursunoni domin tallafa masu tare da yi masu wa’azin su yi hakuri a game da halin da suke ciki a tsare a wannan wuri da Allah Ya jarrabce su na barinsu a wannan wuri domin gyara halayensu idan sun fito daga jarun. Mun bayar da kayan ne domin fursunoni Musulmi da Kirista su yi amfani da su.”
Ya ce: “Ci gaba da dorewar irin wannan aiki sai idan ’yan uwa Musulmi, musamman masu hannu da shuni a ko’ina cikin Najeriya sun yi amfani da dukiyarsu wajen bayar da tallafi a kowane lokaci, ba sai an jira zagayowar shekara ba. Wannan ne zai karfafa mana gwiwa wajen fadada wannan aiki akalla sau 3 a cikin shekara; a maimakon sau daya da muke yi a yanzu.”
Limamin masallacin gidan yari na Kirikiri kuma Jami’in kula da jin dadin fursunoni, Ustaz Abdulrasheed Hamzat da Ustaz Abdullahi Alkawari na JIBWIS, su ne suka shafe awoyi biyu suna yi wa fursunonin wa’azi. Jim kadan bayan kammala wa’azin ne wasu masu hali daga cikin tawagar ta JIBWIS suka fara raba wa daruruwan fursunonin kudi.