An tallafa wa iyalan ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki a Jigawa

Iyalan ’yan sanda bakwai ne suka samu tallafin Naira dubu 500 kowannensu daga Hukumar ’Yan sanda ta kasa a Jihar Jigawa, sakamakon umarnin da rundunar ta kasa ta bayar, cewa a ba iyalan ’yan sandan da suka rasu a lokacin da suke gudanar da aikinsu na kare kasa da lafiyar al’umma. Sauran ’yan sandan kuma […]

An tallafa wa iyalan ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki a Jigawa

Iyalan ’yan sanda bakwai ne suka samu tallafin Naira dubu 500 kowannensu daga Hukumar ’Yan sanda ta kasa a Jihar Jigawa, sakamakon umarnin da rundunar ta kasa ta bayar, cewa a ba iyalan ’yan sandan da suka rasu a lokacin da suke gudanar da aikinsu na kare kasa da lafiyar al’umma.

Sauran ’yan sandan kuma da hukumar ta agazawa sun hada da wadanda suka samu hadari, sakamakon haka suka rasa rayukansu da wadanda aka harbe su yayin yaki da barayi ko mayakan Boko Haram. Sai dai kuma wadanda suka samu hadari na kaddara rundunar ta ’yan sanda su ma ba ta kyale su ba, ta ba su agajin inshora.

Yayin da wadanda suka yi hadari ko suka samu tsautsayin harbin bindiga amma ba su mutu ba, an dauki nauyin duk abin da suka kashe wajan neman lafiyarsu, wadanda su ma tuni aka ba da umarnin a biya su.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, Alhaji Bala Zama a lokacin da ya kira taron inganta rayuwar ’yan sanda da iyalansu a hedikwatar ’yan sandan da ke jihar.

Kwamashinan ya kuma karrama wadansu ’yan sanda biyar da suka yi fice a kan aikinsu saboda hazakarsu da kwarewa. Jami’an sun hada da Sufeto Muhammed Jibrin da Sufeto Dauda Sani da Umar Yakubu da Sajen Iliya Buba da Sajen Sa’idu Jibrin da suke aikin sintiri, suke fafatawa da marasa gaskiya a kan hanyar Birnin Kudu zuwa Gwaram, inda suka samu nasarar kama biyu daga cikin ’yan fashin da suka addabi jama’a a kan hanyar.

A cewar Kwamishina Zama, rundunar ta dauki matakin haka ne da nufin kara wa ’yan sanda masu hazaka kwarin gwiwa, domin su rika dagewa a kan aikinsu na kare lafiya da dukiyar al’umma.

Hukumar ta bayyana sunayen jami’an da iyalansu suka samu tallafi saboda sun rasa mazansu ko ’yan uwansu, wadanda suka hada da Usaini Idi da Shu’aibu Nadabo. Yayin da wadanda suka samu matsala ta hadari kuwa suka hada da Ibrahim Yunusa da Umar Abdullahi da Nantap E. Damulap da Fatima Ibrahim da kuma Jessica John. Yayin da shi kuma Ibrahim D. Wudil zai amfana da tallafin kudin magani daga rundunar ’yan sandan ta kasa.