An tallafa wa kare mai jela a goshinsa

Jami’a cibiyar masu agajin karnuka ta ‘Mac’s Mission’ a jihar Missouri da ke Amurka, sun tsunto wani karamin kare wanda suka radawa suna Narwhal (mai abin mamaki) mai kimanin mako 10 da haihuwa. Wannan karen ya nada jela a goshinsa wanda hakan yasa ya zama wani sabon abu da ba a saba gani ba, halittar […]

An tallafa wa kare mai jela a goshinsa

Lokacin da ake duba karen a asibiti

Jami’a cibiyar masu agajin karnuka ta ‘Mac’s Mission’ a jihar Missouri da ke Amurka, sun tsunto wani karamin kare wanda suka radawa suna Narwhal (mai abin mamaki) mai kimanin mako 10 da haihuwa.

Wannan karen ya nada jela a goshinsa wanda hakan yasa ya zama wani sabon abu da ba a saba gani ba, halittar karen tasa jama’a da dama suka yi ta martani a shafukan yanar gizo. An tsinto karen ne a cikin sanyi lokacin da wadanda suka mallake shi, suka hana shi masauki.

Jami’an sun samu karen da rauni a kafarsa a gefan hanya tare da wani tsohon kare, amma duk jami’an suka hada su tare don taimaka masu.

Bayan jami’an sun wallafa bidiyon yadda karen ke da wannan halitta a goshinsa a shafin Facebook, hakan yasa masu bibiyan shafin suka yi ta martani game da wannan abin al’ajabin da karen yake da shi.

Su dai wadannan jami’an da suke cibiyar ta jihar Missouri, sun shahara ne wajen taimakawa karnukan da basu da gata aka watsi da su suna gararanba a hanya, ko kuma wadanda zasu haihu da wadanda aka ji wa rauni,  ko kuma karnuka masu nakasa, wanda suka ce ba tare da taimakon su ba za su iya mutuwa saboda wahala.

Ita dai wannan jelar yadda ta rika bai wa masu kallon bidiyon da aka wallafa ba ta motsi kamar bata jikin halitta mai rai.

An kai karen asibitin dabbobi, bayan jami’an ceton sun tabbatar da cewa karen ba zai razana jama’a ba. Sai suka fara tunanin mai haddasa fitowar jelar a goshinsa ko kuma an dasa masa ne? Sannan abu muhimmi shi ne ya za a yi jelar ta rika motsi.

Bayan asibitin sun sanya ranar da za a yi binciken lafiyar karen, cibiyar Macs Mission ta wallafa cewa, “ Jelar da take goshin karen ba dasawa aka yi ba da wani abu ba, sai dai kawai halitta ce da tasa karen ya zama na musamman daga cikin sauran halittun karnuka.”

Wani da yake martani a bidiyon karen da aka wallafa, na cewa, amma ba a yi wa karen kwalliyar da ta dace ba, sai daga baya ya yadda da maganar jama’a wajen tabbatar da cewa, wannan karen fa halitta shi aka yi a haka.

Likitan asibitin dabbobin mai suna Dakta Heuring, ya ce a yanzu haka babu wani dalilin cire wannan karin jelar, sai dai nan gaba ana fatan jelar zata rika motsi kamar mai rai.

Wannan halittar karen Narwhal, bai canza masa wani yanayi na kamar mai nakasa ba, yana rayuwa kamar yadda sauran karnuka suke yi.

Jami’an ceton da farko sun yi tunanin cewa, jelar goshin zata iya cutar da karen, amma daga bisani suka fahimci wannan baida matsala a jikinsa.

Daga bisani cikin masu martani wani ya ce, wannan jelar ta karawa karen kyau a fuskarsa, kuma bata cutar da shi.

Wani kuma cewa ya yi, wannan karen dan baiwa ne, duk lokacin da na kalli fuskar karen yana da matukar kyau da sha’awa.