An tallafa wa ’yan sandan Edo da na’urar raba lantarki
Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adam Aliyu Oshiomhole ya ba hedikwatar ’yan sandan jihar kyautar taransifomar lantarki.Gwamnan ya ba da wannan gudunmowar ce a lokacin da ya gano cewa hedikwatar ta ’yan sandan tana fama da matsalar rashin hasken lantarki, wanda ya kai kimanin watanni 15 kuma matsalar hakan ta faru ne saboda injin raba hasken […]
Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adam Aliyu Oshiomhole ya ba hedikwatar ’yan sandan jihar kyautar taransifomar lantarki.
Gwamnan ya ba da wannan gudunmowar ce a lokacin da ya gano cewa hedikwatar ta ’yan sandan tana fama da matsalar rashin hasken lantarki, wanda ya kai kimanin watanni 15 kuma matsalar hakan ta faru ne saboda injin raba hasken lantarki na cibiyar ya gaza yin aiki, domin ya lalace.
Kwamishinan albarkatun ma’adanai na jihar, Mista Saturday Idahen, shi ne ya mika kyautar wannan taransifoma a madadin gwamnan jihar ga hedikwatar ’yan sandan jihar a makon da ya gabata.
A nasa jawabin wajen mika kyautar taransifomar, Kwamishinan ya ce wutar lantarki tana daga cikin abin da za ta taimaka wa batun tsaro: “Hasken lantarki ita ce mabudin tabbatar da tsaro ciki da waje, don haka ya kamata gwamnati ta tabbatar da ’yan sanda suna aiki ba wai a cikin birni kadai ba.” Ya kara da cewa lallai ya ji dadi kwarai da ganin yanzu hedikwatar hukumar ’yan sanda ta samu lafiyayyar tiransifoma, domin wannan abin farin ciki ne kuma abin a yaba wa Gwamnatin Jihar Edo.
Shi kuma da yake karbar wannan gudunmowar, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Chris Ezike ya nuna jin dadi tare da farin ciki, inda ya gode wa gwamnan jihar yana mai cewa: “Muna farin ciki kuma mun gode kwarai da gaske, domin wannan tiransifomar babba ce da za ta kai har mu mika hasken lantarkin zuwa barikin ’yan sanda na Adesuwa; domin su ma a barikin suna fama da matsalar rashin isassar wutar lantarkin.”