An tantance mutum miliyan 1 don yin aikin kidaya —NPC
An dage kidayar da aka shirya yi a watan Mayu, kuma ba a sake sanya ranar da za a yi ba.
Kwamishinar Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) mai wakiltar Jihar Benuwau, Patricia Kupchi, ta ce kimanin ma’aikata miliyan daya aka tantance domin yin aikin kidayar 2023.
An dage kidayar, wadda aka shirya yi a watan Mayu, sai dai har yanzu ba a bayyana ranar da za a yi ba.
- DAGA LARABA: Yadda Kungiyoyin NGO Ke Neman Hana Zaman Aure A Maiduguri
- Na kashe sama da miliyan 80 a girkin da ya sa na kafa tarihi – Hilda Baci
Kupchi, a jawabinta da ta gabatar a wajen wani taro kan yadda aka sake tsara kidayar yawan jama’a da gidaje na 2023 a Makurdi, ta ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a har sai an sanar da sabuwar ranar yin kidayar.
“An kammala daukar ma’aikatan wucin gadi ne kafin sake jadawalin kidayar jama’a ta hanyar tsauraran matakai ta intanet, inda aka tantance ma’aikata kimanin miliyan daya aka kuma gano cewa sun cancanci yin aikin.
“Hukumar ta samu mataimaka na musamman don kidayar 2023. Kimanin na’urori 500,000 aka kai ofisoshin da ke jahohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja domin yin aikin da su,” inji ta.
Kupchi ta ce dage jadawalin ya bai wa hukumar damar kara inganta matakai da tsare-tsare don gudanar da kidayar jama’ar yadda ya kamata.
Ta bai wa ‘yan Najeriya tabbacin kidayar 2023 za ta zamo mafi alfanu ga kowa.