An tarwatsa masu adawa da takarar Shugaban Aljeriya karo na hudu
’Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da takarar neman shugabancin kasar, na Shugaban Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika a karo na hudu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito..Kimanin mutum 100 suka rika daga aluna masu dauke da rubutun da ke nuni da cewa: “Ba mu yarda da karin wa’adin mulki a karo na […]
’Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da takarar neman shugabancin kasar, na Shugaban Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika a karo na hudu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito..
Kimanin mutum 100 suka rika daga aluna masu dauke da rubutun da ke nuni da cewa: “Ba mu yarda da karin wa’adin mulki a karo na hudu ba,” wani rubutun kuwa cewa ya yi, “Ba amince a kaskantar da Aljeriya ba.” An tarwatsa taron mutanen da suka yi gangami a a gaban jami’ar da ke Babban Birnin kasar, inda suka yi artabu da ’yan sanda, kamar yadda daya daga cikin masu zanga-zangar, Hakim Raissi, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP
Shugaba Bouteflika, dan shekara 76 ne, ya kuma dade ba ya bayyana a bainar jama’a, tun bayan da kamu cutar shanyewar jiki a bara. Duk da haka, ana sa ran zai sake lashe wani zabe, ta hanyar amfani da jami’an gwamnati da dukiyar kasa.
Jam’iyyun adawa da dama sun yi kira kan a kaurace wa zaben, inda suka bayyana cewa, tuni aka kammala hada sakamakon zaben.