An tarwatsa masu fasa shago a zanga-zanga a Kano

Jim kadan da fara zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano ne matasan suka yi wa wani kafafen shago dirar mikiya da sunan kwasar ganima

An tarwatsa masu fasa shago a zanga-zanga a Kano

Jami’an tsaro sun tarwatsa gungun wasu matasa da ke kokarin fasa shaguna su kashe kayan jama’a a safiyar Alhamis a Jihar Kano.

Jim kadan da fara zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano ne matasan suka yi wa wani kafafen shago dirar mikiya da sunan kwasar ganima.

Amma jami’an tsaro sun dakile yunkurin sun kuma fatattake su,  duk da cewa matasan sun farfaɗo gilasan shagon.

Yanzu dai komai ya lafa a wurin da abin ya faru a kan Titin Zoo Road, an kuma ci gaba da gudanar da harkoki.

Kotu ta bayar da umarnin bai wa Hamdiyya tsaro

Yadda na taso daga almajiranci na zama shugaban NNPCL – Kyari

Shugaban ’yan sandan Mopol na Legas ya Musulunta a Kano

Mun daidaita tsakaninmu ni da Alpha – G-Fresh