An tarwatsa masu zanga-zangar adawa da dokokin Coronavirus a Faransa

‘Yan sanda sun harba wa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa.

An tarwatsa masu zanga-zangar adawa da dokokin Coronavirus a Faransa

Yadda aka rika sanya hayaki ami sa hawaye

’Yan sanda a Faransa sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da dokokin Coronavirus da mahukunta suka kakaba da zummar dakile yaduwar cutar.

An harba hayaki mai sa hawaye, tare da cin tarar daruruwan mutane a ranar Asabar don tarwatsa ayarin motocin da suka yi yunkurin datse hanya a wata zanga zangar adawa da dokokin dakile cutar Covid-19 wadda suke ganin ta tsananta tsadar rayuwa da suke fuskanta.

Mutanen da suka samu kwarin gwiwa daga abin da direbobin manyan motoci a babban birnin Canada, Ottawa suka yi, sun fito da da yawa daga sassa daban daban na Faransa don gudanar da wannan zanga zanga.

’Yan sandan, wadanda suka haramta zanga zanga, sun yunkura cikin hanzari don taka wa masu kokarin shiga birnin Paris birki, inda suka ci tarar da dama da suka shiga haramtacciyar zanga zangar.

Sai dai fiye da ababen hawa 100 sun samu kai wa ga dandalin nan na Champs-Elysees, inda nan ne ’yan sanda suka harba musu barkonon tsohuwa, abin da ke tuni da zanga zangar masu tufafin ruwan dorawa ta Yellow vex.