An tashi baram-baram tsakanin Gwamnati da kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa

Yunkurin Gwamnatin Jihar Nasarawa na cimma yarjejeniya da kungiyar Kwadago ta Jihar don kawo karshen yajin aikin sai baba ta gani da ma’aikata ke yi a jihar, ya ci tura. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar kuma shugaban zaman tattaunawa a kan yajin aikin daga bangaren gwamnati Mista Joseph Ancho ne ya bayyana haka a lokacin da […]

An tashi baram-baram tsakanin Gwamnati da kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa
An tashi baram-baram tsakanin Gwamnati da kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa

Yunkurin Gwamnatin Jihar Nasarawa na cimma yarjejeniya da kungiyar Kwadago ta Jihar don kawo karshen yajin aikin sai baba ta gani da ma’aikata ke yi a jihar, ya ci tura. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar kuma shugaban zaman tattaunawa a kan yajin aikin daga bangaren gwamnati Mista Joseph Ancho ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Lafiya kan zaman sasantawar da suka yi da kungiyar a ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar.
Shugaban Ma’aikatan ya ce a yanzu gwamnati ta amince ta biya kusan kashi 80 na bukatun ’yan kwadagon da a cewarsa suka hada da gaggauta biyan albashin watan Janairu da biyan kudaden karin girma da alawus-alwasu din ma’aikatan da kudaden da gwamnati ke biya a kowane karshen wata don gudanar da harkokin manyan makarantun jihar da biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi da bai wa bangaren shari’a damar cin gashin kansa da sauransu.
Ya musanta jita-jitar da wasu ke yadawa cewa gwamnati tana shirin rage wa ma’aikatan albashi, inda ya ce gwamnati ba ta taba tunanin haka ba. Ya ce tunda Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya hau ragamar mulki bai taba rike wa ma’aikatan albashi ko da na wata daya ba kuma yana tabbatar da dorewar kyakkyawar dangantaka a tsakanin gwamnatinsa da kungiyar kwadago a jihar. Ya ce abin takaici ne a ce yau kungiyar tana nuna masa rashin imani.
Daganan sai ya yi kira ga ma’aikatan su yi wa Allah su koma bakin aiki su kuma yi la’akari da wahalhalun da al’ummar jihar musamman ’yan makaranta ke fuskanta sakamakon yajin aikin.
Sai dai a bangaren Shugaban kungiyar kwadago ta Jihar Abdullahi Adeka lokacin a ganawarsa da wakilinmu kan batun ya ce har yanzu ba su cimma yarjejeniya da gwamnati ba, ya ce har yanzu gwamnati ba ta biya ko daya daga cikin bukatunsu 21 ba kamar yadda Shugaban Ma’aikatan ya bayyana.