An tashi wasan Najeriya da Ghana babu ci

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta tashi babu ci a wasan da ta fafata da takwararta ta Black Stars ta Ghana, a gasar neman cancanta buga Kofin Duniya da za a yi bana a kasar Qatar. An buga wasan ne da maraicen Juma’a, a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi […]

An tashi wasan Najeriya da Ghana babu ci

Tawagar Super Eagles

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta tashi babu ci a wasan da ta fafata da takwararta ta Black Stars ta Ghana, a gasar neman cancanta buga Kofin Duniya da za a yi bana a kasar Qatar.

An buga wasan ne da maraicen Juma’a, a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi a kasar ta Ghana.

Ana sa rana sake buga wasan a filin wasa na kasa na Moshood Abiola da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Talata, 29 ga watan Maris, 2022, da misalin karfe 6:00 na yamma.

Duk kasar dai da ta samu nasara za ta kasance cikin daya daga cikin jerin kasashe biyar din da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniyar da za a buga a tsakiyar wannan shekarar.