An taso keyar ‘yan Najeriya daga Birtaniya
A shekaranjiya Laraba ne wani jirgin sama dauke da wasu ’yan asalin Najeriya da aka taso keyarsu daga Birtaniya ya sauka a filin jiragen saman Legas, kamar yadda kafar yada labarai BBC ta bayyana.Akasarin mutanen da aka kora sun ce ba su ji dadin hakan ba.daya daga cikinsu ya ce ’yan sandan Birtaniya sun kama […]
A shekaranjiya Laraba ne wani jirgin sama dauke da wasu ’yan asalin Najeriya da aka taso keyarsu daga Birtaniya ya sauka a filin jiragen saman Legas, kamar yadda kafar yada labarai BBC ta bayyana.
Akasarin mutanen da aka kora sun ce ba su ji dadin hakan ba.
daya daga cikinsu ya ce ’yan sandan Birtaniya sun kama shi, kuma ba su bar shi ya dauki ko da tsinke ba kafin su saka shi a jirgi.
Wasu daga cikinsu sun ce ba su da dangi a Najeriya don haka ba su san wurin da za su je ba.
Tunda fari dai wasu kafafen yada labarai ne suka ba da labarin cewa jirgin sama dauke da ’yan Najeriya 500 da aka koro daga birnin Landan bisa keta dokar zama a kasar ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed.
Sai dai jami’an Hukumar Shiga da Fice ta Najeriya ta karyata adadin mutanen da aka koro domin a cewar Kakakin Hukumar Mista Ekpedeme King kasar Birtaniya ta koro mutum 48 ne ba 500 bisa dalilan keta dokar shiga da fice na kasa-da-kasa kuma yawan cin su suna zaune acan ne bayan bizar su ta kare.
A kwanakin baya ne Najeriya ta nuna rashin jin dadinta da sanarwar da Birtaniya ta yi cewa za ta kori ’yan Najeriya 29,000 daga kasar, tana mai cewa bai kamata a kore su ba har sai an bi ka’ida.
Gwamnatin Najeriya dai ta bukaci Birtaniya ta tabbatar cewa mutanen da za ta kora ’yan Najeriya ne kuma suna da koshin lafiyar da za su iya fita daga kasar.