An tilasta wa limamai yin rawa a China
A wani yunkuri na tursasawa da tauye ’yancin addini, mahukuntan kasar China sun tilasta limaman masallatai yin rawa a kan titi tare da yin rantsuwa ba za su koyar da yara addini ba da kuma gaya musu cewa addini na cutar da ruhi a gundumar dinjiang da Musulmi suka fi yawa.Jaridar World Bullentin ta ruwaito […]
A wani yunkuri na tursasawa da tauye ’yancin addini, mahukuntan kasar China sun tilasta limaman masallatai yin rawa a kan titi tare da yin rantsuwa ba za su koyar da yara addini ba da kuma gaya musu cewa addini na cutar da ruhi a gundumar dinjiang da Musulmi suka fi yawa.
Jaridar World Bullentin ta ruwaito a ranar Litinin cewa a lokacin an tilasta limaman Musulmi su rika fadin cewa “Kudin shigarmu na zuwa ne daga CKP ba daga Allah ba.”
Wata kafar labarai ta China ta ce an tara limaman ne a wani dandali da sunan wayar da kai inda aka tilasta su yin rawa da rera kalaman goyon bayan kasar. Kalaman da suka hada da fifita kasar a kan addini kamar cewa, ‘zaman lafiyar kasa ke ba da zaman lafiyar ruhi.’
Kuma an tilasta su gabatar da jawabai da suke shaida wa matasa su guji zuwa masallatai da kuma cewa Sallah tana cutar da lafiyarsu, tare da karfafa musu su rika rawa maimakon yin Sallah.
An kuma umarci malaman makaranta mata su koya wa yara kaurace wa ilimin addini tare da daukar rantsuwar za su daina koya wa yara addini.
Al’ummar Musulmin Uighur dai ’yan asalin Turkiyya ne marasa rinjaye da suka kai mutum miliyan takwas a yankin Arewa maso Yamma na yankin dinjiang. dinjiang wanda masu kare hakkin dan Adam ke kira da Turkestan ta Gabas ya samu ’yancin kai tun 1955, amma yana fama da hare-haren jami’an tsaron gwamnatin China. Kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun sha zargin gwamnatin China da cin zarafin al’ummar Musulmin Uighur a yankin dinjiang da sunan yaki da ta’addanci.
A watan Nuwamban bara an hana yin Sallah a gine-ginen gwamnati, yayin da a watan Agusta birnin Karamay da ke Arewacin dinjiang ya haramta wa matasa masu gemu da ’yan mata masu hijabi shiga motocin gwamnati.
Kafin nan a watan Yuli, China ta haramta wa dalibai yin azumin Ramadan, baya ga yadda hukumomin yankin dinjiang ke kakarin hana ’yan mata Musulmi sanya dan kwali.