An tona asirin sojan sama na bogi

Kwamandan sojan sama, sashin kula da ayyuka na musamman da ke Kalaba, Olusegun Philip ya bayyana wa manema labarai nasarar cafke wani matashi, Abdussalam Isyaka da laifin yi musu sojan gona.Dubun matashin ta cika ne a garin Oron, Jihar Akwa Ibom, bayan da rundunar hadin gwiwa ta sojojin sama da ke aiki a jihar suka […]

An tona asirin sojan sama na bogi
An tona asirin sojan sama na bogi

Kwamandan sojan sama, sashin kula da ayyuka na musamman da ke Kalaba, Olusegun Philip ya bayyana wa manema labarai nasarar cafke wani matashi, Abdussalam Isyaka da laifin yi musu sojan gona.
Dubun matashin ta cika ne a garin Oron, Jihar Akwa Ibom, bayan da rundunar hadin gwiwa ta sojojin sama da ke aiki a jihar suka kawo Kalaba saboda nan ne hedikwata.
Daga cikin abubuwan da aka kama wanda ake zargi da aikata laifin da su, akwai katin shaida na jabu da ke nuna shi sojan sama ne da kuma makamai da suka hada da wuka da adda da kuma ankwa, tare da barkonon tsohuwa.
Aminiya ta ji ta bakin wanda ake zargin, inda ya ce shi dan asalin Jihar Kano ne. A lokacin da yake bayyana dalilan da suka sanya shi fadawa wannan harka, ya ce: “Ni direba ne da ke aiki da rundunar sojojin sama da ke Legas, amma daga bisani a kore ni aiki saboda ’yan wasu laifuffuka da aka same ni da su lokacin ina aiki.” Ya ci gaba da cewa a wurin wani abokinsa soja ya je ya samo kayan da wasu lokuta yakan kira shi suna fita yin cuwa-cuwa bayan sun tashi aiki. Ana dauka ta sojan haya ma, in bayar da kariya wajen sabga ta aure ko ta wani biki ko walimar suna da sauransu” inji shi.