An tono akwatunan gawa masu shekara 2,500 a Masar
Har yanzu rubutu da launukan akwatunan da aka yi da katakai ba su lalace ba
Masu binciken kayan tarihi sun tono akwatunan gawa masu shekara 2,500 a wata makabarta da ke Giza ta kasar Masar.
Ministan Harkokin Yawon Bude Ido da Kayayyakin Tarihi, Khaled al-Anany, ya sanar da cewa an tono akwatunan gawar ne dinke a cikin wani kabari mai zurfin mita 11.
“Gano wadannan akwatinan shi ne mafi yawan akwatinan gawa da aka taba samu a makabarta guda tun da aka samu na Asasif Cachette’’, inji ministan.
An gano akwatinan gawa na mutane da guda 30 a watan Oktobar 2019, a makabartar Asasif da ke yankin Luxor na kasar ta Masar.
Ministan tare da Babban Sakataren Hukumar Zartarwa ta Kayan Tarihin (SCA) Mostafa Waziri, sun ziyarci wurin a lokacin tonon kaburburan ranar Lahadi.
“Abubuwan da aka samu a Saqqara sun hada da akwatinan gawa na katakai da launukansu da rubutunsu ba su lalace ba duk da shekaru 2,500 da suka kwashe a karkashin kasa”, inji Waziri, wanda ya jagoranci masu binciken kayan tarihin kasar ta Misra a Saqqara.
Ya shaida wa kamafanin dillancin labarai na Xinhua cewa har yanzu ba su tantace yawan akwatinan gawa da suka zakulo ba balle su san sunayen masu su.
Sai dai ya ce za su ci gaba da tonon makabartar da kuma tantace sunayen masu akwatunan gawar nan da kwanaki masu zuwa.
“Tono zai ci gaba a makabartar kuma muna kyautata zaton gano wasu abubuwa da suka jibanci kaburburan da kalar akwatinan gawa na katako da kuma matsayinsu”, inji shi.
Ministan ya kuma ce, sun lura tun daga farkon tonon makabarta cewa dukkanin akwatunan gawar a dinke suke, kuma ba a taba bude su ba tun da aka binne su.