An tono gawa lafiyarta lau bayan shekara 20 da binne ta

An tono gawar marigayi Sarkin Bukur na Biyu, Malam Suleiman wanda aka fi sani da Baba Sarki lafiyar lau, bayan shekara 20 da rasuwarsa. Sarkin ya rasu ne a daidai lokacin da ake fama da cikin rikicin Jos a shekarar 2001 inda aka binne shi a filin Makarantar Firamaren LEA da ke kusa da bankin […]

An tono gawa lafiyarta lau bayan shekara 20 da binne ta

Gawar Sarkin Bukur na Biyu

An tono gawar marigayi Sarkin Bukur na Biyu, Malam Suleiman wanda aka fi sani da Baba Sarki lafiyar lau, bayan shekara 20 da rasuwarsa.

Sarkin ya rasu ne a daidai lokacin da ake fama da cikin rikicin Jos a shekarar 2001 inda aka binne shi a filin Makarantar Firamaren LEA da ke kusa da bankin First Bank daf da ofishin Gidan Waya (Post Office) a Bukur, a Jos, fadar Jihar Filato.

A lokacin Kungiyar Izala ce ke amfani da wurin don yin Sallar Juma’a amma a kwanankin baya sai aka samu sabani a tsakanin bangarori biyu na Izala, inda bangarorin suka amince a tone gawarwakin da aka binne a filin makarantar a canja musu wuri.

Bangarorin na Izala sun kuma amince a ba wani dan kasuwa wurin ya gina shagunan da za su rika kawo musu kudin shiga.

Kuma a ranar 18 ga Afrilun bana ce aka tono gawar Baba Sarki don a sake mata wuri kusa da Fadar Sarkin Bukur na yanzu.

Lokacin da aka tono gawar Sarkin Bukur na Biyu

Wadanda aka tono gawar a idanunsu sun ce, an samu gawar Baba Sarki kamar yadda aka binne ta, babu abin da ya canja.

Hakan dai yana nufi gawar da aka tono tana nan cikakkiyarta kamar ba a dade da binne ta ba, lamarin ya ba jama’a da dama a Jos mamaki.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC