An tono gawar mawaki Mohbad don binciken musabbabin mutuwarsa
’Yan sanda sun ce nan ba da jimawa ba za a fara binciken
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar da tono gawar marigayi mawaki Ilerioluwa Oladimeji Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.
An dai hako gawar mawakin ne ranar Alhamis domin gudanar da zuzzurfan bincike kan musabbabin mutuwarsa a makon da ya gabata.
- An maka kamfanin Google a kotu saboda rashin iya kwatance ga direba
- Ban ga dalilin da ’yan Najeriya za su rika rayuwa cikin talauci ba – Tinubu
Kakakin Rundunar a Jihar, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a dandalin X (Twitter a da), inda ya ce nan ga da jimawa ba za a fara binciken.
“An kammala aikin tono gawar. Nan ba da jimawa ba za a fara aikin binciken musabbabin mutuwar #JusticeForMohad #Justice4Mohbad,” kamar yadda Benjamin ya wallafa.
A wani labarin kuma, tuni Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya gayyaci Hukumar Tsaro ta DSS da ta shiga cikin bincike kan mutuwar mawakin.
Mutuwar Mohbad, mai shekaru 26 ta janyo ce-ce-ku-ce matuka musamman a kafafen sada zumunta na zamani a ciki da wajen Najeriya.
Kazalika, an gudanar da zanga-zanga a jihohin Legas da Oyo da Delta, don neman a binciki musabbabin mutuwar ta shi.