An tono kaburburan ‘yan ci rani a Malesiya
A shekaranjiya Laraba ne ‘yan sanda a kasar Malesiya suka tono kaburra a wani daji mai iyaka da kasar Thailand. ’Yan sandan dai sun ce mutane sun rasu ne sakamakon matsananciyar yunwar da suka yi fama da ita lokacacin da masu safararsu suka tsare su. Kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san […]
A shekaranjiya Laraba ne ‘yan sanda a kasar Malesiya suka tono kaburra a wani daji mai iyaka da kasar Thailand.
’Yan sandan dai sun ce mutane sun rasu ne sakamakon matsananciyar yunwar da suka yi fama da ita lokacacin da masu safararsu suka tsare su. Kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san adadin mutane da wannan matsalar ta shafa ba. Har ila yau, ana zargin cewa ‘yan ciranin sun mutu ne a hannun masu garkuwa da su.
Galibinsu dai ‘yan ci-ranin Musulmi ne ‘yan kabilar Rohingya daga kasar Myanmar da Bangladesh. Kuma sun dauracewa kasarsu ne saboda rikici da ya yi kamari tun shekarar 2012.
Akwai kuma wadansu dubban ‘yan ci rani daga wurare daban-daban suke ketara tekun Andaman zuwa kasar Malaysiya domin neman abin sa wa a baka. Kuma ana zargin cewa wasu na garkuwa da su domin neman kudi.
kasar Thailand dai tana yaki da batun fataucin ‘yan ci rani kuma an yi yakinin cewa shirin da take yi ya bar dubban ‘yan ci ranin cikin halin ni-’ya-su, a cikin jiragen ruwa, a tekun Andaman.