An tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
An fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, bayan an kwashe kwana uku ana mummunan barin-wuta tsakanin dakarun da ke goyon bayan Shugaba Salba Kiir da Mataimakinsa Riek Machar.Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, kamar yadda BBC ta bayyana.Birnin Juba ya yi tsit, kuma babu rahotannin shawagin […]
An fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, bayan an kwashe kwana uku ana mummunan barin-wuta tsakanin dakarun da ke goyon bayan Shugaba Salba Kiir da Mataimakinsa Riek Machar.
Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, kamar yadda BBC ta bayyana.
Birnin Juba ya yi tsit, kuma babu rahotannin shawagin jiragen yaki masu saukar ungulu ko tankokin yaki a kan hanyoyin birnin.
Ranar Litinin ne dai Salba Kiir da Riek Machar suka sanar da cewa za su tsagaita wuta, wacce ta fara aiki da misalin karfe uku a agogon Najeriya da Nijar.
Taho-mu-gamar da aka yi tsakanin bangarorin biyu tana barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.
Wannan fada dai ya sanya tsoro kan barkewar wani sabon rikici, da alamar cewa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015 za ta rushe.
A shekarar 2011 ne Sudan ta Kudu ta zama kasa mai cin gashin kanta daga Sudan, bayan an kwashe shekara da shekaru ana yakin-basasa.