An tsare barayi 2 kan satar buhun zobo 10 a Jigawa

An kama wadanda ake zargin dauke da wasu karafa da adduna da suke fasa shagunan al’umma.

An tsare barayi 2 kan satar buhun zobo 10 a Jigawa

Jami’an Hukumar Sibil Difens a Jihar Jigawa, sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi da satar buhun zobo guda 10 a jihar.

Kakakin rundunar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a Karamar Hukumar Hadeja.

Ya ce, an kama su ne a ranar Lahadi 21 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 8:30 na safe a unguwar Gawuna da ke Hadeja.

A cewarsa an cafke su dauke da buhu 10 na zobo wanda ake zargin na sata ne.

Mahmud, ya ce bincikensu ya nuna cewa wadanda ake zargin sun hada baki tare da fasa shagon wani Alhaji Yusuf Idris da ke Gawuna a Karamar Hukumar Hadeja.

Ya ce sun yi awon gaba da buhu 10 na zobo.

Amma kakakin ya ce, an kwato buhun zobon gaba daya, wanda darajarsa ta kai Naira N362,250.

Kazalika, ya ce an kama barayin da wasu karafa da adduna da suke amfani da su wajen fasa shagunan al’umma a yankin.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan