An garkame dan majalisa bisa zargin garkuwa da mutane
Wata kotu ta tsare dan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina Ala ta Yamma a Jihar Binuwa bisa zarginsa da fashi da kuma garkuwa da mutane. Kotun Majistaren ta tsare dan Majalisar Dokokin Jihar Binuwai Jonathan Agbidye a gidan yarin ne bayan an gurfanar da shi a ranar Juma’a. Mai Shari’a Isaac Ajim ya ba da […]
Wata kotu ta tsare dan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina Ala ta Yamma a Jihar Binuwa bisa zarginsa da fashi da kuma garkuwa da mutane.
Kotun Majistaren ta tsare dan Majalisar Dokokin Jihar Binuwai Jonathan Agbidye a gidan yarin ne bayan an gurfanar da shi a ranar Juma’a.
Mai Shari’a Isaac Ajim ya ba da umarnin tsare Agbidye dan jam’iyyar APC ne tare da wanda ake zarginsu tare.
Dan sanda mai gabatar da kara Fidelis Ogbobe ya shaida wa kotun cewa a ranar 22 ga watan Mayun 2018 an yi fashin wata motar a-kori-kura kirar Hilux da wasu kayan cikinta da bakin bindiga a hanyar Katsina-Ala zuwa Tordonga a Karamar Hukumar Katsina-Ala.
Ya ce wadanda ake zargi da kwace motar motar mallakin shirin kula da lafiya na Apin, sun kuma yi garkuwa da jami’an lafiyar wanda kowanne daga cikinsu babban laifi ne.
Jami’in ya ce daga baya ‘yan sanda suka kama Agbidye da abokin harkarsa a Makurdi da motar sun canza mata lamba.
Mutanen biyu da wasu biyu da suka tsare, a cewarsa, sun hada baki ne kuma ‘yan fashi ne da kuma garkuwa da mutane karkashin gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Terwase Akwaza (Ghana) wanda ake nema ruwa a jallo.
Zaman kotun bai kai ga sauraron bayanan bangarorin biyu ba.
Lauya mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa ana kan binciken mutanen don haka ya nemi karin lokaci domin a kammala.
Lauyan wadanda ake bai ja da bukatar ba amma ya ce nan gaba zai gabatar da bukatar karbar su beli.
Mai Shari’a Ajim ya dage sauraron karar zuwa 12 ga watan Oktoba 2020, yayin da aka wuce da dan majalisar da abokinsa zuwa Babban Gidan Yarin Tarayya da ke Makurdi.