An tsare dan sanda don ya zagi alkali a kotu

Kotun Shari’ar Musulunci ta 7 da ke Fagge Waje a birnin Kano ta bayar da umarnin a tsare wani dan sanda bisa samunsa da laifin zagin alkali a cikin kotu.dan sandan mai suna Abubakar Yusuf Cika Aiki ya shiga harabar kotun a sukwane a daidai lokacin da ake gudanar da shari’a yana zage-zage inda yake […]

An tsare dan sanda don ya zagi alkali a kotu
An tsare dan sanda don ya zagi alkali a kotu

Kotun Shari’ar Musulunci ta 7 da ke Fagge Waje a birnin Kano ta bayar da umarnin a tsare wani dan sanda bisa samunsa da laifin zagin alkali a cikin kotu.
dan sandan mai suna Abubakar Yusuf Cika Aiki ya shiga harabar kotun a sukwane a daidai lokacin da ake gudanar da shari’a yana zage-zage inda yake neman sai kotun ta mayar masa da matarsa da ’ya’yansa.
Aminiya ta gano cewa a shekarun baya ne kotun ta raba auren dan sandan da matarsa inda ta damka sha’anin rikon ’ya’yan a hannun mahaifiyarsu kamar yadda Musulunci ya tanada.
A lokacin da dan sandan ke ta zagin alkalin ne sai alkalin ya ba ’yan sandan kotun umarnin su kama Abubakar amma sai Abubakar din ya dunkule hannu yana shirin kai duka ga duk wanda ya kusance shi.
An dai yi nasarar kama Abubakar a karshe ta hanyar gayyato wani dan sanda inda suka hadu da sauran ma’aikatan kotu suka yi wa Abubakar taron dangi inda suka dauke shi cak suka kai inda ake tsare wadanda ake tuhuma na kotun suka kulle shi a ciki.
Alkalin Kotun Mai shari’a Nasir Abba Magashi ya bayar da umarnin tsare dan sandan tsawon mako guda a kurkuku inda zai fuskanci shari’a.